A ci gaba da gudanar da bikin cika shekaru 61 da haihuwar wanda ya kafa Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP (LEADERSHIP Group Limited), marigayi Sam Nda-Isaiah, mukarrabai sun yi waiwaye kan mashahuran hikimominsa da gudummawar da ya bayar ga ci gaban al’umma a bangaren siyasa da kuma kiwon lafiya.
Mukarraban sun kuma yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Sam Nda-Isaiah lambar yabo ta kasa.
Sam Nda-Isaiah wanda ya rasu a ranar 11 ga Disambar 2020, sakamakon gajeriyar jinya, bayan kasancewarsa dan kasuwa, har ila yau ya kasance jigo a jam’iyyar APC.
Mashahuran sun bayyana kyawawan halayen marigayin, masanin harhada magunguna, da suka ce yana da hangen nesa kana haziki ne a fagen siyasa mai kishin kasa. Abokansa da fitattun ‘yan Nijeriya sun lura cewa Sam Nda-Isaiah ya yi imani da kasancewar Nijeriya kasa daya dunkulalliya, da kishin ci gaban matasa da shugabanci nagari kuma ya yi tsayuwar daka a kan bin ra’ayinsa tare da hada karfi da karfe da sauran kwararru wajen korar jam’iyyar PDP daga kan karagar mulki a 2015.
A cewarsu, girmama wanda ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da shugabanci nagari a Nijeriya abin alfahari ne ga gwamnatin APC, musamman ma a lokacin gwamnatin Buhari.
Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jaridu na Nijeriya (NPAN), kuma shugaban Kamfanin Media Trust Ltd, mawallafin Jaridun Daily Trust, Malam Kabiru Yusuf, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta karrama Marigayi Sam Nda-Isaiah da lambar yabon da za a rika tunawa da shi bisa gudummuwar da ya bayar a Nijeriya.
Shugaban NPAN ya bayyana hakan ne a sakonsa na murnar zagayowar ranar haihuwar Marigayi Sam Nda-Isaiah wanda aka gabatar wa LEADERSHIP ranar 1 ga Mayun 2023.
Ya ce, “’Yan’uwa da abokin arzikinmu, a yau muna tunawa da zagayowar ranar haihuwar Sam da ya cika shekara 61 wanda mutuwa ta dauke mana shi.
“A lokacin da yake ganiyarsa, ya bayar gudummawa da yawa a fannoni da dama na rayuwar kasarmu masu matukar muhimmanci. Ya kasance masanin harhada magunguna, marubuci, mawallafin jarida kuma dan siyasa. Ya ratsa wadannan fannoni cikin kwarewa da hazaka wanda ya bambanta shi da sauran mutane.
“Mu da muka san shi an bar mu da zurfafa tunani. Ya kamata kasar nan wanda ya kula da ita da yi mata hidima ta girmama shi da lambar yabon da mutane za su dinaga tunawa da shi, domin wannan shi ne fahimtarmu.”
Ita ma zababbiyar sanatan Abuja a karkashin Jam’iyyar LP, Hajiya Ireti Kingibe, ta bayyana cewa Sam Nda-Isaiah ya kasance dan kishin kasa mara tsoro kuma mai hakuri, wanda a ko da yaushe yake yi wa kasa fatan alheri, sannan ya yi matukar yin kokari wajen zaburar da al’umma da kuma wayar da kan jama’a.
“Soyayyarsa ga Nijeriya ta haskaka ko’ina. Na tuna yadda ya yi tsayin daka wajen tabbatar da kyautatuwar shugabanci a Nijeriya.
“Sam ya kasance mai yawan goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari. Don haka, ba na jin dadin cewa Sam ba a ba shi lambar yabo ta kasa bayan mutuwarsa ba, saboda ayyukansa ga wannan kasa. Babu wanda ya fi sanin irin cancantar wannan lambar yabo kamar shugabannin wannan gwamnati,” in ji shi.
Har ila yau, wani abokin marigayin, shugaban gudanarwa na makarantar nazarin kasuwanci ta Netherlands (BSN) a Nijeriya, Farfesa Lere Baale, ya ce Sam Nda-Isaiah ya kasance mai ban mamaki wanda ake tuna mashahuran hikimominsa na “Big Ideas” a Nijeriya, ya kasance fitaccen dan jarida, dan kasuwa kuma dan siyasa.
Baale wanda ya ce, Nda-Isaiah ya bar wani wagegen gibi da ba za a iya cikewa ba a daidai wannan lokacin bisa la’akari da halin da Nijeriya take ciki a halin yanzu, idan aka lura da irin gudummuwar da ya bayar a kasar nan ya cancanci a karrama shi da lambar yabo ta kasa.
“Ya kuma kasance mai taimakon jama’a wanda ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban bangarori da dama na al’ummar Nijeriya, musamman a fannin ilimi da kiwon lafiya. A matsayinsa na dan jarida, Sam Nda-Isaiah ya barranta daga irin rahotannin da ake wallafawa na yau da kullum, ya mayar da hankali ne kan matsalolin da ke damun Nijeriya,” in ji Baale.
A nasa bangaren, babban jami’in kamfanin Heights Access Nigeria Limited, Harry Thomas-Odey, ya bukaci jam’iyyar APC da ta rika tunawa da hikimomin Marigayi Sam Nda-Isaiah na “Big Ideas,” wanda a nan ne APC ta samu damar dunkulewa wuri guda.
“Sam ya kara wa APC armashi, domin ya kasance mai fafutuka da ya jaddada bukatar jam’iyyun adawa su hade kansu su kulla kawance saboda hambarar da jam’iyyar PDP a karagar mulki.”
Daya daga cikin makusantan Sam Nda-Isaiah kuma tsohon Manajan Darakta na LEADERSHIP Group Ltd, Abdul Gombe ya ce, “Karrama Sam da lambar yabo bayan mutuwarsa zai yi matukar kyau. Duk wanda ya san Sam ya san shi da kishin kasar nan. A ko da yaushe yana sha’awa a yi abubuwa daidai a Nijeriya,” in ji Gombe, yana mai karawa da cewa, “Sam ya yi imani da shirin Buhari.”
Har ila yau, dan takarar shugabancin jam’iyyar APC a zaben fid da gwani, Mohammed Saidu Etsu, ya yi kira da babbar murya a kan karrama Marigayi Sam Nda-Isaiah da lambar yabo ta kasa a matsayin mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen samun nasarar gwamnati mai ci a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
A cewar jigon na jam’iyyar APC, “Ba za a iya misalta irin gudunmawar da Sam ya bayar ga dimokuradiyyar Nijeriya ba, kuma ya dace a karrama shi da lambar yabo bayan mutuwarsa. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin cewa dimokuradiyya ta samu ci gaba a Nijeriya, kuma abin da ya bari zai ci gaba da zaburar da al’ummomi masu zuwa gaba.”
A halin da ake ciki kuma, wata sanarwa da iyalan Nda-Isaiah suka fitar na cikar zagayowar ranar haihuwarsa shekara 61 bayan rasuwarsa, ta tuna cewa Marigayi Sam Nda-Isaiah ya kasance bango ga iyalansa wanda ya samar da kishin kasa, ko da kuwa akwai barazana a gare shi.
Sanarwar da Abraham Nda-Isaiah ya sanya wa hannu ta ce, “Sam ya kasance babban bango ga iyalinsa da na kusa da shi, domin sun kasance da shi suka dogara. Ya yi kokari don habaka rayuwar al’umma. Ya yi rayuwa ta hidimta wa al’umma tare da tunanin habaka rayuwar duk wadanda suke rabe da shi.
“A matsayinmu na iyalai, muna kewarsa amma mun gode wa Allah da ya yi rayuwa mai tasiri da kuma abubuwan da ya bari. Ya kasance shekara mai wahala ba tare da Sam ba a cikinmu. Amma mun san yana can yana jin dadi sosai. Ba za mu yi bakin ciki ba a ranar haihuwarsa bayan mutuwa, da sanin cewa watakila yana rayuwa mai kyau a can. Muna kewarsa sosai, amma mun san za mu sake kasancewa tare da shi. Muna murna da zagayowar ranar haihuwasa.”
An haifi Sam Nda-Isaiah a garin Minna, Babban Birnin Jihar Neja a ranar 1 ga Mayun 1962. Ya halarci makarantar ilementare ta UNA kafin ya koma makarantar cocin Christ da ke Kaduna a 1968, inda a nan ne ya kammala karatunsa na firamare.
Ya halarci kwalejin gwamnatin tarayya da ke Kaduna daga shekarar 1974 zuwa 1979. Daga nan kuma ya yi karatun fannin harhada magunguna a Jami’ar Obafemi Awolowo, sannan ya yi aikin bautar kasa a babban asibitin Jihar Ekiti a shekarar 1984.
Ya kasance tsohon dalibi na makarantar Lee Kuan Yew a jami’ar kasar Singapore.
Sam ya fara aikinsa a matsayin mai bayar da magunguna a asibitin kwararru na Kano kafin ya koma babban asibitin Minna. Ya yi aiki a kamfanin Pfizer Products Limited daga 1985 zuwa 1989.
Ya kasance dan jarida mai kishin kasa wanda ya shahara wajen rubuta mukala mai taken, “Last Word” da mutane ke tururuwan karantawa. Ya fara wannan shafi ne a matsayin marubuci na musamman kuma mamban kwamitin editocin jaridar Daily Trust, kafin ya kafa LEADERSHIP da kudaden da ya samu daga wajen kaddamar da tarin mukalun da ya wallafa a shekarar 2001. Kafin LEADERSHIP ta zama cikakkiyar jarida, Sam ya fara wallafa ta a matsayin fallayen LEADERSHIP CONFIDENTIAL, wanda ta samu karbuwa daga al’umma, musamman tsakanin jami’an difilomasiyya da manyan ‘yan siyasa da kuma ‘yan kasuwa.
Sam ya nuna jarumtaka ta musamman ta hanyar rubuce-rubucen da yake yi, wanda hakan ya sa jaridar ta shahara kuma a lokuta da dama ta samu sabani da gwamnati, musamman a zamanin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua da Olusegun Obasanjo.
A sakamakon gudunmawar da ya bayar a harkar yada labarai, Sam Nda-Isaiah ya zama mamba a kwamitin gwamnatin Jihar Kano don farfado da jaridar The Triumph mallakar gwamnatin jihar. A 2003, ya kasance babban jami’in watsa labarai na yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kasance mamba na cibiyar nazarin Asiya da cibiyar habaka Hong Kong. A shekarar 2019, an nada shi mamba a kwamitin gudanarwa na jami’ar Baze da ke Abuja.
A shekarar 2015, Sam Nda-Isaiah ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya a zaben fid da gwani na jam’iyyar APC tare da taken yakin neman zabe na ‘Big Ideas’. Sai dai bai samu damar samun tikitin takarar shugaban kasa ba.
Mai martaba Etsu Nupe na yanzu Alhaji Yahaya Abubakar, ya nada shi sarautar Kakaki Nupe. Sannan Oba Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi Odundun ya ba shi sarautar ‘Aare Baaroyin’ na masarautar Akure.
Mutum ne mai nuna kwazo a kan duk abin da yake nema, ya jajirce wajen aiwatar da manufofin da ya yi imani da su, ya kasance babban dan kishin kasa wanda ya yi imani da hadin kan Nijeriya.