A yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana jin radadin kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
Sai dai kuma ya ce gwamnatinsa ta cika mafi yawan alkawuran zaben da ya yi wa ‘yan Nijeriya a zaben 2015 da na 2019.
Shugaban ya ce har abada yana godiya ga ‘yan Nijeriya da suka zabe shi domin ya tafiyar da al’amuran kasar a madadinsu, bayan an yi masa gwaji da gazawa, kamar yadda ya yi nadamar cewa wannan shi ne jawabinsa na ranar samun ‘yancin kai na karshe a matsayinsa na shugaban kasa.
Da yake bayar da bayanin yadda ya gudanar da mulkinsa a cikin shekaru bakwai da suka gabata, Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen dakile matsalolin tsaro da suka addabi Nijeriya a farkon gwamnatinsa.
“Sabbin siffofin da suka saba wa kasarmu sun fara bayyana musamman na garkuwa da mutane, cin zarafi, kisan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, fashi da makami, wanda jami’an tsaron mu ne ke magance su.
Ya ce, “Ina jin irin radadin da ‘yan Nijeriya ke ciki kuma ina tabbatar muku da cewa juriya da hakurinku ba za su kasance a banza ba domin wannan gwamnati na ci gaba da daukar matakai tare da karfafa jami’an tsaro don ba su damar tunkarar duk wani kalubalen tsaro.”
Ya bayyana cewa a farkon gwamnatinsa a shekarar 2015 ya samar da kudaden da hukumomin tsaro ke bukata wanda kuma aka inganta a wa’adinsa na biyu a shekarar 2019 domin samun damar shawo kan matsalolin tsaro.
‘Yan Nijeriya da dama na fatan kalaman na shugaba Buhari su kasance ta yadda wasu yankuna za su sarara daga hare-haren da ake yi ba dare ba rana.