A halin yanzu har an cika shekara 9 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari makarantar sakandire ta ‘yan mata da ke garin Chibok a Jihar Borno inda suka sace tare da yin garkuwa da ‘yan mata 276 daga dakunan kwanansu, daga cikin wadannan ‘yan makaranta har yanzu da akwai sauran ‘yan mata 98 a hannun ‘yan ta’addan.
Sace ‘yan matan makarantar Chibok da aka yi a ranar 14 ga watan Afrilu 2014 shi ne na farko a fadin duniya, inda aka sace tare da yin garkuwa da ‘yan mata masu yawa haka a lokaci daya Kamar yadda aka yi zato lamarin ya dauki hankalin al’umma duniya da shugabanni a bangarori da dama na rayuwar al’umma da suka hada da na siyasa, kasuwanci, wasanni da sauransu inda aka yi kira da nuna bukatar a tabbatar da an ceto su ba tare da wata matsala ba.
- Ban Da Masaniya Kan Yi Wa Shugaban NIS Jere Ritaya – Aregbesola
- Sin Ta Samarwa Kasashen Waje Tallafin Ayyukan Likitanci Ba Tare Da Sharudan Siyasa Ba
Saboda tabbatar da an ceto ‘yan matan ne har aka kaddamar da gangamin tiwita mai suna ‘hashtag, #BringBackOurGirls (#BBOG)’ wanda ya mamaye sassan duniya daga baya aka haifar da wata kakkaffar kungiya mai suna Bring Back Our Gilrs wadanda ‘yan gwagwamarmaya Aisha Yesufu da Hadiza Bala, da tsohuwar ma’aikaciyar Bankin Duniya da kuma Ministar Ilimi, Dakta Oby Ezekwesili suka jagoranta, sun yi watanni suna gabatar da zaman dirshan da zanga-zanga don matsawa gwamnati lamba don ta zafafa kokarin da take yi na ceto ‘yan matan.
Irin halin ko in kula da gwamnatin Goodluck Jonathan da kuma yadda wasu jami’an gwamnatin suke yi ta nunawa a kan lamarin ‘yan matan Chibok ya sanya al’umma suka kasa gamsuwa da kokarin da gwamnatin take yi na ganin an ceto ‘yan matan, wanda hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sanya Shugaba Jonathan ya kasa lashe zaben hankoronsa na darawa karagar shugabancin Nijeriya karo na biyu a shekarar 2015.
Haka kuma duk da alkawarin da gwamnatin Shugaba Buhari da ta biyo bayan na Jonathan ta yi na ceto yaran ba a cimma nasarar hakan ba har zuwa yanzu. Gwamnatin ta samu nasarar ceto ‘yan mata 100 a lokutta biyu, daban-daban ta hanyar tattauanawa da kuma amfani da salon bani gishiri in baka manda da wadanda suka sace yaran, duk kuwa da cewa, gwamnati ta karyara cewa, an bayar da kudi a yayin karbar ‘yan matan.
A tsawon wannan lokacin wasu ‘yan matan sun samu nasarar tserewa daga wadanda suka sace su ko kuma yayin da aka kashe ‘yan ta’addan da ke rike da su wasu kuma sojoji da jami’an tsaro ne suka ceto su a farmakin da suke kaiwa a yankin arewa maso gabas. Da yawa daga wadanda aka ceto duk sun zama matan aure wasu ma sun haihu, ‘yan ta’addan ne ke aurensu. Gaba daya zuwa yanzu a kwai ‘yan mata 98 da ba a san halin da suke ciki ba zuwa yanzu, duk da kuma ana fargabar cewa, wasu ‘yan matan na iya mutuwa a musayar wuta da ake yi a tsakanin juami’an tsaro da ‘yan ta’adda da kuma wsasu dalilai masu yawa da za su iya kai wa ga mutuwar wasu daga cikin ‘yan matan.
Akwai labari mai kara karfin gwiwa da ke nuna cewa, wasu daga cikin ‘yan matan da aka ceto sun koma makaranta a cikin gida da wasu ma a wasu kasashen duniya, wasu sun shiga jami’ar ‘American Unibersity of Nigeria (AUN), Yola, a karkashin tallafin karatu na gwamnatin tarayya. A watan Mayu na shekarar 2022, daya daga cikin ‘yan matan mai suna, Lydia Pogu, ta kammala karatun ta na digirin digirgi daga wata jami’ar kasar Amurka, mai suna ’Southeastern Unibersity, USA, yayin da wasu daga cikin su suka kammala digiri daga wasu jami’o’in.
Tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok dubban wasu ‘yan matan a wasu makarantun su fuskanci cin zarafi da dama a lokutta daban-daban tun daga yadda aka sace wasu ‘yan matan a makarantar Dapchi da ke Jihar Yobe a shekarar 2018 zuwa na baya-bayan nan da aka yi ranar 7 ga watan Afrilu 2023, inda ‘yan bindiga suka sace yara 80 a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Hukumar kulawa da al’amura gaggauwa na kanana yara ta bayyana cewa, daga shekarar 2014, an samu cin zarafin yara har sau 2,400 inda abin ya shafi yara fiye da 6,800 a yankin arewa maso gasas, cikin cin zarafin yaran sun hada da yadda ‘yan ta’adda ke shigar da yara kanana harkokin ‘yan bindiga da kuma yadda ake samun labarin sace yara fiye da 693 a ayyukan ta’addanci da aka yi ma fiye da 675 a sassan kasar nan.
Mummunan tasirin ayyukan ta’addan a kan harkar ilimi yana da girman gaske zai kuma ci gaba da samar da matsalar zuwa wani lokaci mai yawa a nan gaba. Hukumar Kula da Malaman makaranta ‘Teachers’ Registration Council of Nigeria (TCN)’ sun bayyana cewa, sun bayyana cewa a tsakanin shekarar 2009 da 2022, an kashe malamai fiye da 2,295 a hare-haren da aka kai musu an kuma tarwatsa rayuwar malamai 19,000 haka kuma an kulle makarantu 1,500 saboda matsalar tsaro abin da kuma ya kai ga lalata makarantu fiye da 910 a hare-haren ta’addanci da aka kai.
Abn takaici kuma a nna shi ne, yanzu shekara 9 ke nan bayan da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok, amma har yanzu babu alamar za a dakatar da sace-sacen ‘yan makaranta a Nijeriya, yan ta’adda a yankin arewa maso gabas, arewa ta yamma da arewa ta tsakiya na ci gaba da cin karen su babu babbaka, jihohin Zamfara, Jigawa, Niger, Kaduna da Kebbi na daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren ta’addanci a kan makarantu wanda hakan na nuna cewa, shirin nan na gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro a makarantun mu ya sha ruwa kenan.
A ‘yan watannin da suka wuce yayin da ake hada-hadar yakin neman zaben 2023 babu wani magana da aka ji daga masu takara a kan halin da ‘yan matan Chibok ke ciki, yanzu kuma gashi wa’adin gwamnatin Buhari yana gab da karewa babu wata magana na yadda za a ceto sauran ‘yan makarantare Chibok 98 da suka rage a hannun ‘yan ta’adda da ba a san halin da suke ciki ba. A matsayinmu na gidan jarida muna kira ga gwamnati mai kamawa da ta tabbatar da ta yi tsare-tsaren da zai ga ceto wadannan ‘yan mata don kasance da iyalansu, haka kuma akwai bukatar su samar da tsarin kare makarantu da ‘yan makaranta daga fadawa hannun ‘yan ta’adda.