A yayin da ake shirin shiga sabuwar shekarar Musulunci a watan na Al- Muharram, wadda ke nuna kawo karshen shekara, tawagar mabiya Malaman addinin Kirista a jihar Kaduna, sun taya mabiya Addinin Musulunci da ke a fadin kasar nan murnar shirin shiga sabuwar shekara.
Kazalika, sun shawarce su da su kara yin kaimi wajen yin addu’oin samun zaman lafiya da hadin kai.
- Gwamnonin Arewa Sun Yi Wa Dahiru Mangal Jajen Rasuwar Matarsa
- Gwamnan Bauchi Ya Rushe Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomi
Fitaccen Fasto a jihar, Yohanna Buru ne, ya isar da sakon malaman mabiya addinin kirista a yayin da tawagar matasa Musulmi suka kai masa ziyara a gidansa da ke unguwar Sabon Tasha a Kaduna.
Matasan sun kai masa wannan ziyarar ne, bisa nufin kara karfafa dankon zumunci a tsakanin matasa mabiya addinin biyu da kuma kara wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ziyarar ta su dai, ta zo ne daidai da zagayowar bikin ranar abota ta duniya da aka saba gudanarwa a duk ranar 30 ga watan Yulin kowacce shekara.
Buru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana ranar shiga sabuwar shekarar ta Musulunci a matsayin ranar hutu ga Musulmi don Musulmi su gudanar da shagulgulan bakin ranar, mussaman ganin tuni, wasu jihohin da ke a kasar, tuni suka ayyana ranar a matsayin ranar hutu ga Musulmin da ke a jihohin su.
Sai dai, ya koka ganin cewa, Musulmin kasar nan, za su shigo cikin watan na Muharram dai dai da lokacin da ake ci gaba da samun tashin gwauron Zabi na kayan masarufi a kasar.
Ya yi kira ga Musulmi da su tallafa wa marasa karfi, marayu da mata zawarawa da kayan abinci a lokacin gudanar da bukukuwan bikin zagoyowar shekarar ta Musulunci.
Shi ma a na sa jawabin a lokacin ziyarar Fasto John Joseph, ya nanata mahimmancin zaman lafiya a daukacin fadin kasar nan.
Kazalika, ya yi kira, musamman ga matasa mabiya addinan biyu, da su gujewa furta kalaman kiyayya, su kuma rungumi dabi’ar son zaman lafiya a tsakaninsu.
Shi kuwa, shugaban kungiyar matasan Musulmi reshen jihar, Mallam Gambo Abdullahi Barnawa, ya godewa malaman mabiya addinin Kirista kan taya Musulmi murnar shiga sabuwar shekara, inda ya yi addu’ar kara dangon zumunci a tsakanin mabiya addinin biyu da ke fadin Nijeriya.