Babban Hafsan rundunar tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cewa ma’aikatar sarrarafa makamai ta Nijeriya (DICON), ta taimaka wajen samar wa rundunar kayayyakin aiki.
Kayayyakin sun sun hada da motocin yaki da kayayyakin sulken da rundunar soji ke bukata na aikin samar da tsaro a kasar.
- Birtaniya Za Ta Wahala Idan Likitocin Nijeriya Suka Bar Kasar – Ministan Lafiya
- Ban Taɓa Karɓar Cin Hanci Ko Taɓa Ƙuɗin Ƙananan Hukumomi Ba – Shekarau
Janar Musa, ya bayyana hakan ne, a taron kwanaki biyu da aka soma yau a Abuja na cikar ma’aikatar ta DICON shekaru 60 da kafuwa.
Nasarorin da ma’aikatar ta samu ba ya rasa nasaba da sanya hannu kan dokar ma’aikatar ta shekarar 2023 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu a kai a watan Nuwamban 2023.
Idan ba a manta ba, ya bai wa ma’aikatar damar cimma manyan nasarori gami da fadada ayyukanta domin ci gaban Nijeriya.
Tun da fari dai, Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa assasa ma’aikatar sarrafa makaman a shekarar 1964 alamu ne na cin gashin-kai da Nijeriya ta tabbatar, wajen harkokin tsaro da ci gaban kasa.
Ma’aikatar ta zama silar nasarar ayyukan tsaro a kasar tare da fara sayar wa kasashen ketare makamai.
A shekarun da ta kwashe, ma’aikatar ta yi namijin kokari wajen shimfida kyakkyawar manhajar samar da tsaro a kasar.
Sannan ta taimaka wa rundunar tsaron Nujeriya da kayayyaki, domin saukaka ayyukansu na tsaro.
Ministan, ya bayyana cewa ko shakka babu, a karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ma’aikatar za ta ci gaba da samar da nasarori a wannan fannin tsaro.
A nasa jawabinsa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya ce shekaru 60 da kafuwar ma’aikatar sarrafa makamai alamu ne na tabbatar da tsantsar kishin kasa a harkar tsaro.
Shekaru 60 da suka gabata, ma’aikatar DICON ta himmatu ne, wajen sarrafa makamai da kayan yaki domin taimaka wa rundunar tsaro da sauran ma’aikatun tsaron Nijeriya a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya a kasa baki daya.
Shugaban ya ce, hakika ma’aikatar DICON ta taka muhimmiyar rawa a samar wa dakarun Nijeriya da kayan aiki a lokacin yakin basasa domin tabbatar da kasantuwar Nijeriya kasa daya mai cin gashin-kanta.
Shugaba Tinubu, ya kara yin kira ga jagororin ma’aikatar da su kara himma da fadada tunani ga samar da kayayyakin zamani a shirin gwamnati na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.
Har wa yau, ya yi kira ga ‘yan kasa su taimaka su bayar da goyon baya ga nasarar ma’aikatar.
Daga bisani, shugaban ya kaddamar da sabon tambarin ma’aikatar tare da littafi na musamman da aka wallafa na cikar DICON shekaru 60 da kafuwa.
Taron, ya samu halartar ministoci, shugabannin tsaro da jami’an kasashen waje da kamfanoni da manazarta harkokin tsaro da ‘yan jarida.