Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha, domin wakiltar Nijeriya a Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na Biyu kan Tsarin Abinci, wanda zai gudana daga 27 zuwa 29 ga Yuli, 2025.
Sanata Shettima zai kasance tare da shugabannin duniya domin tattauna batun gyaran tsarin samar da Kofi da kuma halartar wasu taruka na gefe da suka shafi tabbatar da tsaron abinci a Najeriya.
A cewar mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, taron zai ba da dama wajen tantance ci gaban da aka samu tun bayan taron farko na shekarar 2021, da kuma ƙarfafa ayyukan da ke nufin gina tsare-tsaren abinci masu ɗorewa da jurewa ƙalubale.
Haka zalika, Shettima zai shiga wasu tarukan gefen babban taron, inda za a nuna misalai na ainihi kan yadda ake sauya tsarin abinci, da musayar sani (ilimi) da haɓaka haɗin gwuiwa, da kuma haɗa ƙarfi don cimma mafita bisa shaidar bincike da fasaha.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da za a gudanar a gefen taron shi ne zagayen tattaunawar ministoci kan kuɗin jama’a, kasuwanci da saka hannun jari mai yawa, domin saurin tafiyar da sauyin tsarin abinci a nahiyar.
A wani bayani da tawagar Nijeriya ta gabatar kwanan nan, Shettima ya bayyana burin Nijeriya: ta zama jagora a tsarin abinci na nahiyar Afrika, yin amfani da haɗin gwuiwar ƙasa da ƙasa bisa fifikon gida, da kuma haɓaka tsarin da ke ƙarƙashin jagorancin kamfanoni masu zaman kansu.
Taron na bana an shirya shi ne tare da haɗin gwuiwar Majalisar Ɗinkin Duniya, da gwamnatin Habasha da Italiya. Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa zai dawo gida bayan kammala ayyukan taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp