Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Abuja bayan halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80, wanda ya gudana a birnin New York da kuma wasu taruka da ya yi a Jamus a madadin Shugaba Bola Tinubu.
Mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa a lokacin ziyarar mako guda, Shettima ya gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda ya buƙaci a yi gyare-gyare a Majalisar, ya kare buƙatun Afirka kan ma’adanai masu darajar dala biliyan 700, tare da ƙarfafa dangantaka da Birtaniya, Gidauniyar Bill Gates, da sauran abokan hulɗar ƙasa da ƙasa.
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kama Ɓarayi A Jihar Neja
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗi Kan Yiwuwar Aukuwar Ambaliya A Wasu Jihohi
Haka kuma, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya gana da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, wanda ya yaba da yunƙurin Nijeriya na neman kujerar dindindin a Majalisar Tsaro ta Duniya.
A wata ganawa ta daban, Shettima ya gabatar da damar zuba jari a shirin sauya makamashi a Nijeriya mai darajar dala biliyan 200 ga masu saka jari daga ƙasashen waje.
Kafin ya zarce Jamus, ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya da ke ƙasashen waje cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da haɗa su cikin manufofi da shirye-shiryenta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp