Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ci gaba da jan ragamar teburin La Liga ta bana bayan ta bai wa abokiyar hamayyar ta Real Madrid tazarar maki takwas karo na biyu a kakar nan.
Barcelona ta doke Sebilla 3-0 a wasan mako na 20 da suka kara a filin wasa na Nou Camp ranar Lahadi kuma hakan ya sa kungiyar da Dabi ke jan ragama ta hada maki 53 ta ci gaba da zama a matakin farko, ita kuwa Real Madrid ta biyu tana da maki 45.
A wasan da aka buga na mako na 20, Barcelona ce ta hada maki uku a tsakanin kungiyoyi shidan teburin babbar gasar ta Sifaniya wanda hakan yake nufin akwai ci gaba sosai a kungiyar.
Cikin kungiyoyin shidan farko Atletico Madrid ce ta tashi 1-1 da Getafe ranar Asabar, Celta Bigo ta je ta doke Real Betis 4-3 ranar Lahadi sannan a ranar Lahadin Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Mallorca da wanda Balladolid ta je ta ci Sociedad 1-0 a karshen mako.
Barcelona ta ci kwallo ukun ta hannun Jordi Alba da Gabi da kuma Raphinha a wasan da ta yi kuma kawo yanzu saura wasanni 18 kenan maki 54 suka rage a karkare wasannin babbar gasar ta Sifaniya ta bana.
Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki takwas, ko a iya cewa watakila kungiyar na kan hanyar lashe gasar La Liga na kakar nan duba da irin tafiyar wahainiyar da Real Madrid take yi?
A tarihin gasar ta La Liga, duk kungiyar da ta bayar da tazarar maki takwas ko fiye da haka, bayan buga wasa 20 ita ce kan lashe kofin shekarar kuma karo takwas a baya da Barcelona ta ja ragamar teburin La Liga, bayan wasa 20 ta kuma bai wa Real Madrid tazarar maki takwas ko
fiye da hakan, ita ce ta lashe kofin.
Ga jerin kakar da Barcelona ta yi wannan bajintar
Kakar wasa ta 1997 zuwa 1998 da kakar wasa ta 1998 zuwa 1999 da kakar wasa ra 2004 zuwa 2005 da kakar wasa ta 2005 zuwa 2006 da kakar wasa ta 2008 zuwa 2009 da kakar wasa ta 2010 zuwa 2011 da kakar wasa ta 2012 zuwa 2013 da kakar wasa ta 2015 zuwa 2016 da kakar wasa ta 2017 zuwa 2018 da kuma kakar wasa ta 2018 zuwa 2019.
Da yake kwallon kafa ce alkaluma kan iya canjawa a kowanne lokaci, kuma komai zai iya faruwa musamman a kokarin lashe kofin kakar wasan da muke ciki ta 2022 zuwa 2023.