A satin da ya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta tabbatar da cewa tsofaffin ‘yan wasanta guda biyu, Ahmad Musa da Shehu Abdullahi sun koma kungiyar domin buga kakar wasa ta 2024 zuwa 2025.
Sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Abubakar Isa Dandago, ya fitar a shafinsa na Facebook, ta kara da cewa ‘yan wasan guda biyu sun koma kungiyar ne bayan kammala kulla yarjejeniya da shugabannin kungiyar kuma tuni ma sun buga wasan da kungiyar ta samu nasara a kan Sunshines Stars da ci 2-0 a ranar Lahadin da ta gabata a gasar firimiyar Nijeriya.
- Shin Usman Abdalla Zai Iya Dawo Da Martabar Kano Pillars?
- Kokarin Farfado Da Ilimi: Gwamnan Kano Ya Zama Gwarzo A Tsakanin Gwamnoni
Ahmad Musa, mai shekara 31 a duniya ya buga wasa a kungiyar ta Kano karo biyu a baya, inda ya buga wasa a Kano Pillars a kakar wasa ta 2009 zuwa 2010 da kuma shekara ta 2021 kuma ya yi bajinta sosai a wannan lokacin.
Shima dan wasa Shehu Abdullahi kuma, dan asalin Jihar Sakkwato, wanda ba shi da kungiya tun shekarar 2023, ya buga wasa a kungiyar a shekara ta 2012 kuma shi ma kamar Ahamd Musa, ya wakilci tawagar Super Eagles ta Nijeriya a wasanni daban-daban.
Sai dai kafin Ahmad Musa ya koma Kano Pillars, zakarun gasar Firimiyar Nijeriya, Rangers international, sun nemi ya koma kungiyar amma tsohon kyaftin din na Super Eagles ta Nijeriya, ya fi son buga wa Kano Pillars wasa.
A kakar wasan Ahmed Musa ta farko a Kano Pillars a Shekarar 2009, ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallo a raga a gasar Firimiyar Nijeriya, inda ya kammala gasar da kwallaye 18 wanda hakan ne ya ja hankalin kungiyar BBB Benlo ta kasar Netherlands ta dauke shi.
Har ila yau, Ahmad Musa ya buga wasa a kungiyoyin CSKA Moscow ta kasar Rasha da Leceister City ta Ingila, sai kuma Al Nassr ta kasar Saudiyya kafin ya koma kasar Turkiyya inda nan ma ya buga kakar wasa guda daya.
Shin Zai Taimakawa Kano Pillars?
A wasansa na farko a kungiyar ta Kano Pillars, Ahamd Musa ya zura kwallaye biyu, sannan ya barar da fanareti a wasansa na farko bayan ya dawo kungiyar ta Pillars, a wasan da ‘SAI MASU GIDA’ ta doke Sunshine Stars da ci biyu da nema a filin wasa na Muhammad Dikko da ke
Jihar Katsina a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoban shekarar 2024 kuma wasan shi ne wasa na biyar na gasar Firimiyar Nijeriya na kakar wasa ta 2024 zuwa 2025.
Dan wasan ya zura kwallonsa ta farko a minti hudu da fara wasa, sannan ya kara jefa kwallo ta biyu a minti shida bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai dai saura kiris Musa ya samu nasarar cin kwallo uku rigis a wasan, amma ya yi rashin nasara, inda ya barar da bugun fanareti a minti na 70 a wasan.
Da yake bayyana farin cikinsa, Ahmed Musa ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “na yi farin cikin dawowa Kano Pillars. Ina godiya ga dukkan ma’aikatan kungiyar da abokan wasana da masu horar da ‘yanwasa bisa wannan damar da suka ba ni. Sannan magoya bayannmu da ma duk wadanda suka zo kallonmu, muna godiya. Zura kwallo biyun nan da na yi somin-tabi ne,” in ji shi.
A shekarar 2009 da ya fara buga wasa a Kano Pillars, Ahamd Musa ya zura kwallaye 18 ciki n wasanni 25 da ya buga kafin ya tafi kungiyar kwallon kafa ta BBB Benlo ta kasar Netherland da ke buga babbar gasar kasar.
Sannan ya sake dawowa a shekarar 2021 bayan ya bar kungiyar Al Nassr ta Saudiya, inda ya buga wasanni 8. Sai kuma wannan kakar da ya dawo, bayan ya bar kungiyar Sibasspor ta Turkiyya a shekarar 2024.
Tuni masana suke ganin dawowar Ahamd Musa za ta taimakawa kungiyar musamman wajen zura kwallo a raga kasancewarsa kwararre ne a wannan fannin tun da a baya an ga yadda ya nuna bajinta a gasar ta Nijeriya da ma irin kokarin da ya yi a kungiyar BBB Benlo da CSKA Moscow ta kasar Rasha.
Sannan zuwansa Kano Pillars zai taimaka wa matasan ‘yan wasan gaba na kungiyar wajen koyar iya zura kwallo a raga tare kuma da koyon dabaru kala-kala wajen iya sarrafa kwallo a yadi na 18 da ma irin gudun da ake bukatar dan wasan gaba ya dinga yi wajen neman zura kwallo a raga.
Ba ma iya ‘yan wasan gaba ba, su kansu ragowar ‘yan wasan kungiyar za su samu kwarewa sosai kasancewar Ahamd Musa ya kware sosai saboda ya buga wasa a manyan kungiyoyi a Nahiyar Turai, sannan kuma ya buga wasa da manyan ‘yan wasa a duniya ciki har da Leonel Messi a gasar cin kofin duniya da Nijeriya ta buga da Argentina.
Shi ma dan wasa Shehu Abdullahi zai taimakawa ‘yan wasan kungiyar ta Kano Pillars saboda yadda ya buga wasa a Nahiyar Turai da ma tawagar Super eagles ta Nijeriya, sannan daukar atisayen da za su yi da ragowar ‘yan wasa zai sake bude tunanin ragowar ‘yan wasa.
Dawowar Ahamd Musa da Shehu Abdullahi Kano Pillars ba iya Kano Pillars zai taimaka ba, har da gasar Firimiya baki daya saboda kwararru ne wadanda suka buga wasa a Nahiyar Turai sannan kuma hakan zai bude hanyar wasu ‘yan wasan na Nijeriya da suke buga wasa a Turai su dinga dawowa suna taimaka wa kungiyoyi na gida domin bunkasa gasar cikin gida tare
kuma da samun kudin shiga ga kungiyoyi da ita kanta hukumar da ke kula da shirya gasar.
Kungiyar Kano Pillars dai ba ta buga wasanninta a gida Jihar Kano, yanzu tana buga wasa ne a filin wasa na Muhammadi Dikko dake jihar Katsina a matsayin gidanta, saka makamakon gyara da ake yi a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a Kano, idan har kungiyar ta koma buga wasa a Kano ana ganin abin zai fi armashi.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko fara wasan da kafar dama zai ta dore bisa la’akari da yadda a baya ya koma kungiyar kuma ya buga mata wasanni 8 ba tare da cin kwallo ko daya ba.