• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Inganta Lafiya: An Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,213 A Zamfara

by Leadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na uku na Shirin Inganta Lafiyar al’umma Kyauta, inda aka duba mutane sama da 2,213.

Shirin na musamman da aka fara a watan Yulin bara, an samu nasarar duba lafiyar mutane masu fama da amosanin ido, gwaiwa, yoyon fitsari da aikin musamman tare da wayar da kan mutane sanin hanyoyin kauce wa kamuwa da cututtuka domin kiwon lafiyar su.

  • Gwamnan Zamfara Ya Raba Wa Makarantu 250 Kayan Karatu Da Fitilu Masu Amfani Da Hasken Rana A Jihar
  • Gwamnatin Zamfara Za Ta Gina Tashar Motocin Tilera Biyu A Birnin Gusau

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa an duba lafiyar mutane sama da 2,213 a yayin shirin a matakin farko da na biyu da na uku.

A cewar sa, kashi na uku ya kasance tsakanin ranakun 23 zuwa 25 ga watan Fabrairun 2024.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ƙaddamar da wani shirin inganta lafiyar jama’a kyauta domin bayar da tallafin kiwon lafiya ga mabuƙata. Shirin yana ba da magani kyauta ga mutanen da ke fama da yanayin lalurar rashin lafiya ta yau da kullum kamar su amosanin ido, amosanin mara, gwaiwa da yoyon fitsari.

LABARAI MASU NASABA

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

“Baya taimakon kiwon lafiya, shirin yana ilimantar da jama’a game da muhimmancin kiyaye lafiya da walwala. Wannan yunƙuri mataki ne mai kyau na inganta lafiya da jin daɗin al’umma gaba ɗaya.

“Ya zuwa yanzu an yi amfani da na’urorin zamani a shirin inganta lafiyar mutane 2,213 don ba da kulawa ta musamman ga majinyata daga karkara da birane, wanda ya ƙunshi ƙananan hukumomi 14 na jihar. Wannan tsarin ya bai wa marasa lafiya a wurare masu nisa damar samun kulawar kiwon lafiya da suke buƙata daga ƙwararrun likitoci.

“Shirin, a dukkan matakai, an samu masu lalurar gwaiwa 876, amosanin ido 931, da masu yoyon fitsari 84.

“Cibiyoyin da aka ware domin wayar da kan jama’a, sun haɗa da Babban Asibitin Gusau, Babban Asibitin Sarki Fahad, Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura, kuma za a tura dukkan waɗanda cutar tasu ta yi tsanani zuwa ga babban asibitin Tarayya da ke Gusau.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Labarai

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI
Manyan Labarai

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
Next Post
Matakin Kona Kai Da Sojin Amurka Ya Dauka Ya Diga Ayar Tambaya Ga ‘Yan Siyasar Amurka

Matakin Kona Kai Da Sojin Amurka Ya Dauka Ya Diga Ayar Tambaya Ga ‘Yan Siyasar Amurka

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.