Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ministoci 44 a Majalisar Zartarwa ta tarayya da Gwamnoni 28, za su fara bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu da wa’adinsu zai kare.
Bayyana Kadarori ga dukkanin masu mukaman gwamnati wajibi ne, kuma Hukumar Da’ar Ma’áikata ta ce a shirye ta ke za ta fara ba su fom domin su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara da wa’adin su zai kare.
- Saurin Farfadowar Tattalin Arzikin Sin Yana Kara Habaka Ci Gaban Yankin Asiya Da Duniya Baki Daya
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Kisan Basarake Da Garkuwa A Neja
Wadanda za su karbi wannan fom din su ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni 28 da ministoci 44 da hadiman su, ‘yan majalisar dokokin kasa da na jihohi, da shugabanin kananan hukumomi kamar yadda aka tsara a kundin tsarin mulkin kasar.
Masana sun ce a karkashin sashe na 172 zuwa 209 na kundin tsarin mulki Najeriya ya zama dole ga dukkan ma’aikaci ko da karamin ma’aikaci ne ko kuma babban ma’aikaci, matukar dai kana karban kudi daga baitulmalin gwamnati, to ya zama tilas mutum ya bi wannan umarnin.
Masana sun ce ganin cewa ana iya take dokar ya sa aka kafa Kotun hukunta ma’aikata, wacce aka fi sani da CCB ko kuma Code of Conduct Bureau a turanci.
Mainasara ya kara da cewa anan ne ake hukunta duk wanda aka same shi da laifin sabawa dokokin aiki wanda hukumar da’ar ma’aikata ke sa ido akai idan mutum ya saba.