• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Nijeriya Na Yaki Da Talauci A Duniya

by Sulaiman
3 years ago
Talauci

Talauci lamari ne da miliyoyin al’umma ke fuskanta a sassan duniya. Wannan ne babban dalilin da mutane fiye da 100,000 suka yi gangami a garin Paris na kasar Faransa a ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 1987 don tattaunawa tare da dubi ga mutanen da ke fama da tsananin talauci a duniya.

Rana ce da aka ware don fadakar da al’umma duniya a kan bukatar samar da hanyoyin kawo karshen talauci ta duk hanyar data fito.

  • Matakan Da Ake Dauka Don Kauce Wa Karancin Abinci A Nijeriya –Ministar Jin Kai

Rana ce da ake nazari don samar da hanyoyin fitar da dimbin al’ummar da ke fuskantar talauci da dukkan abubuwan da sukan taso sakamakon taualci a cikin al’umma wadanda suka hada da tashe-tashen hankali, cututtuka da rashin muhalli.

Al’ummar duniyna amfani da lokacin don karfafa tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin mutane da rayuwa ke a cikin talauci da kuma al’umma duniya gaba daya. Ta anan ne ake samun yanayin tattaunawa da sauraron matane masu fama da talauci don fahimtar cikakken halin da suke ciki tare da tattauna yadda za a tallafa musu.

Amma a daidai wannan lokacin mun damu matuka a kan irin barnar da annobar cutar Korona ta yi wanjen kara masu fama da talauci, da tsananin gurbacewar muhalli da kuma abubuwan da yakin Rasha da Yukrain ya haifar wa duniya da kuma yadda lamarin ya haifar da matsananciyar matsalar rashin abinci, a halin yanzu muna fuskantar karanci abinci mafi girma da aka taba fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

Wadannan matsalolin sun kawo cikas ga hanyoyin samar da abinci a wasu lokutta hanyoyin samar da abincin sun kan kulle ne gaba daya, kuma gashi matsaliolin sai kara ta’azzara suke yi, al’umma da dama na cigaba da fuskantar rashin abinci, Talakawa ne suka fi fuskantar wannan matsalar domin kuwa wuraren samun abinci su duk sun bushe a inda kuma ake iya samun abinci yana da tsadar gaske.

A bayyane lamarin yake cewa, al’murra sun rude, iyalai da dama basa iya ciyar da kansu ba wai maganar cin abin mai gida jiki ba, a ma dai samu abinci da za a ci. Abin da ke faruwa sakamakon rashin cin abinci mai gina jiki shi ne cutar yunwa da cututtuka masu tsanani a cikin al’umma, wannan kuma ya fi tsanani ne a tsakanin yara kanana don kuwa karancin abinci ya zama wani makami da ke cutar da yaran talakawa.

Yawan ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki da za su ci da rashin kayan sawa da kuma matsugunai yana karuwa ne a kullum garin Allah ya waye. Wannan abin takaici ne in aka lura da dimbin albarkatun kasa da Allah ya hore mana wannan sai dai ace babu cikkakiyar damuwa ne da rashin sanin yakamata.

Abin kura a kan lamarin talaucin da ake fuskantar Nijeriya shi ne na yadda a duk shedkara ake jin gwamnati ta ware dimbin kudade da sunan yaki da talauci amma kuma al’amarin a kullum sai kara kazancewa yake yi.

Wannan Jaridar ta lura da cewa, duk ikirarin da wannan gwamnatin ke yi na cewa ta fitar da al’ummar Nijeriya fiye da Miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekara 10 amma har yanzu Nijeriya na nan rike da kambunta na hedikwatar talauci na duniya, inda ake da fiye da mutum miliyan 93.9 da ke rayuwa a cikin talauci.

Amma dai gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, shirin nan na fitar da mutum miliyan 100 daga kangin talauci zai tabbata ne daga shekarar 2030, inhar dukkan masu ruwa da tsaki suka bayar da tasu gudummawar yadda yakamata. Wannan dai da kamar wuya, in har gwamnati ta kasa yakar cinhaci da rashawa wadda ke ta kara ta’azzara a kullum.

A shekarar 2019, gwamnatin tarayya ta yi watsi da wani rahoto inda aka ayyana Nijeriya a matsayin hedikwatar talauci a duniya duk kuwa da shugabannin duniya kamar Firayministan Birtaniya Theresa May, ta kara jaddada wannan matsayar.

Daga baya an bayyana mana cewa, Shugaba Buhari zai mayar da hankali a yaki da talauci a zangonsa na biyu a ofis. Amma a yanzu kusan saura wata 7 zuwa karshen wa’adinsa na biyuu amma babu wata kwakwarar hujja da ke nuna cewa, abubuwa sun inganta a kan yadda suke a shekarar 2019. Maimakon haka ma al’ummura sun kara tabarbarewa ne, tun daga lamarin tsaro ga shi kuma matsalar ambaliyar ruwa da ta addabi sassan kasar nan na cigaba da wahalar da al’umma.

Tabbas za a iya magance talauci, ba bin da ba zai iya yiwuwa ba ne. daya daga cikin hanyoyin magance talaucin shi ne sanya talakawa a cikin tattauanwar fito da hanyoyin magance talaucin da kuma karfafa tattalin arziki da samar da hanyoyin aikin yi ga al’ummar Nijeriya, haka kuma dole a yi maganin banbancin da ake nunawa a tsakanin jinsin maza da mata, yana kuma da matukar muhimmanci a inganta cibiyoyin al’umma, wannan tabbas zai matukar kawa karshen talauci a tsakanin al’ummar duniya gaba daya.

Muna kira ga gwamnatin tarayya ta tabbatar da sanya tsare-tsaren yaki da talauci a cikin tsarin ayyyukanta tare da kuma tabbatar da ana aiwatar da tsarin ba tare da bata lokaci ba, ta haka ne ‘yan Nijeriya da dama za su samu fita daga kangin talauci. Haka kuma yakamata gwammati ta zuba jari a harkokin kasuwanci a yankunan karkara wanda ta haka al’umma gaba daya za su amfana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
Kurar Sauya Fasalin Kudi:  ‘Mahaukatan’ Sayen-sayen Da Masu Boye Kudi Ke Yi

Kurar Sauya Fasalin Kudi: ‘Mahaukatan’ Sayen-sayen Da Masu Boye Kudi Ke Yi

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Talauci

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.