Shugaban Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya (NPA), Mohammed Bello-Koko, ya bayyana cewa, an bullo da shirin hada kan yadda ake tafiyar da tashoshin jiragen ruwan Nijeriya ne don samu cin cikakkiyar gajiyar arzikin cikin tekun kasar nan.
Bello-Koko ya bayyana haka ne a yayin gudanar da taron Kungiyar Albarkatun Teku na Duniya (IMO) karo na 33 da ke gudana a birnin Landan.
- NASENI Ta Dukufa Kere-kere Domin Kawo Saukin Rayuwa A Nijeriya –Khalil
- CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024
Bello-Koko ya ce, wannan sabon salon zai hada kan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tashoshin Ruwan Nijeriya, hakan kuma zai karfafa tattalin arzikin kasa da tsaron jiragen ruuwa da kayayyakin da ake shigowa da su a tekun kasar nan.
Ya kuma nuna kwarin gwiwarsa na cewa, Nijeriya za ta cimma wa’adin da hukumar IMO ta bayar na a hada ayyukan tashoshin jiragen ruwan kasar nan nan da shekarar 2025, kamar dai yadda aka ayyana wa mambobin kungiyar.
Shugaban na NPA wanda yana cikin tawagar Ministan Albarkatun teku, Adegboyega Oyetola, da babban sakataren ma’aikatan, Dakta Magdalene Ajani, ya kara da cewa, hukumar za ta samar da hanyoyin saukaka mu’amalar kasuwanci da Nijeriya ta tashoshin jiragen ruwan Nijeriya.