A hukumance a ranar Laraba aka fara yakin neman zaben jam’iyyu a Nijeriya, wanda hakan zai bai wa jam’iyyu siyasa damar tallata ‘yan takarkarunsu.
Sai dai duba da yanayi da halin da kasar nan ke ciki, ya sanya jaridar LEADERSHIP Hausa, ta shirya shiri na musamman a ‘Twitter Space’ don tattauna yadda za a magance komawa gidan jiya.
- Gwamna Bello Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sarkin Lokoja
- Bazan Daukaka Kara Ba, Na Amince Da Hukuncin Kotu Akan Mazabar Yobe Ta Arewa —Lawan
Akwai matsaloli masu tarin yawa da suka shafi Nijeriya wanda suka hadar da matsalar tsaro, hauhawar farashin kayayyakin masarufi, tabarbarewar ilimi da sauran tarin matsololi.
Wadannan matsaloli na daga cikin abubuwan da ‘yan siyasa za su yi amfani da su wajen yi wa ‘yan Nijeriya alkawura, wanda irin wannan wasu ‘yan siyasar suka yi a baya sannan suka kasa cika alkawuran da suka dauka.
Don guje wa fada wa irin wannan tarko, Dakta Yahuza Getso, wanda malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma masani ne kan al’amuran yau da kullum, ya samu damar shiga shirin kai tsaye, sannan ya yi fashin baki kan abubuwan da masu kada kuri’a ya kamata su yi.
Matasa Su Yi Taka-Tsantsan Da ‘Yan Siyasa
Malamin ya yi bayanin kan yadda ya kamata mutane musamman, matasa su yi taka-tsantsan da gujewa shiga sabgar da ‘yan siyasar da za su amfani da wasu wajen aikata miyagun laifuka musamman a lokutan yakin neman zabe da ma lokacin zaben.
“Matasa su ne kashin bayan al’umma yana da kyau su gujewa bin ‘yan siyasa saboda kar a yi amfani da su wajen yin barandar siyasa.”
Shi ma daga na shi bangaren shugaban dalibai Nijeriya, Usman Umar Barambu, ya nuna bacin ransa kan yadda ‘yan siyasa suka yi kunnen uwar-shegu game da yajin aikin da ASUU ke yi. Ya ce suna da kwararran matakin da za su dauka a lokacin babban zaben 2023.
Kowa da Ranarsa, Za A Zo Ranarmu
A matsayina na shugaban daliban Nijeriya, ina baka tabbacin cewar bana za ta zama daban da kowace.
Dole ne zamu zauna da kowanne dan siyasa don jin ta bakinsa kan irin abubuwan da ya tanadar mana; musamman abin da ya shafi noma, ilimi, tsaro, ayyukan yi ga matasa da sauransu.
Idan aka duba ‘yan siyasar nan musamman ‘yan takarar shugaban kasa ba wanda bai rike wani mukami a baya ba don haka, za mu yi waiwaye don ganin irin abin da ya yi sannan mu yi tunanin zabar wanda ya fi kowannensu cancanta.
Mu Ne Za Mu Gyara Kasar Nan
Mu ne muka fi kowa yawa a kasar nan, saboda muna da adadin dalibai wadanda suke Nijeriya da wadanda suke waje, muna da dalibai mutum miliyan 41. Mu ne zamu gyara Nijeriya kuma zamu bada mamaki domin za a fafata da mu.
Gwamnatin Buhari Ta Gaza Shawo Kan Matsalar Tsaro
Dakta Getso, ya kara da cewa “‘Yan takarkaru da suma fito ya kamata su fito su yi rantsuwa, cewar abin da suka yi alkawari za su cika.
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza shawo kan matsalar tsaro duk da cewar kowa ya san inda wadannan masu aikata laifukan suke, dole ne a kawo karshensu, wanda ni na san inda suke kuma gwamnati ta san na san inda suke.
‘Yaki da cin hanci da rashawa, ya kamata a yi amfani da wuka daidai inda ya dace a yanka, don zartar da hukuncin da ya dace.
Daukar hukunci a kan duk wanda aka samu ya aikata daya daga cikin abubuwan dana lissafa, wanda in dai ba a yi haka ba zai yi wahala ba a sake komawa gidan jiya ba.
Shi ma wani da ya halarci shirin, ya ce abu ne mai kyau a ce mutane sun sa hankali kan kowace matsala da ta addabi kasar nan, don tantance dan takarar da ya dace su zaba.
Matara Global Ventures, tsokaci ya yi kan yadda ‘yan Nijeriya ya kamata su fahimci zamantakewa mai kyau da zaman lafiya.
Ya Kamata A Hana ‘Yan Siyasa Amfani Da Matsalar Rashin Tsaro A wajen Yakin Neman Zabe
Nahar Ishaq, cewa ya yi bai kamata ‘yan siyasa su yi amfani da matsalar rashin tsaro a wajen yakin neman zabe ba, inda ya bukaci a yi doka a hana ‘yan siyasa amfani da yanayin matsalar ta rashin tsaro. Ya ce a baya an yi irin hakan kuma babu wani sauyi da aka samu.
Dakta Getso, ya kara yin karin haske kan matsalar rashin tsaro bayan da aka masa tambaya game da gwamnatin shugaba Buhari, inda ya ce gwamnatin Buhari za ta iya magance kashi 60 zuwa 70 na matsalar tsaro.
“Ya kamata a yi doka musamman akan abin da shafi masu damara da suke aikata laifuka, wanda ba a wuce kwana 40 sai an samu wani jami’an tsaro da ya aikata laifi, gwamnati ba ta iya karya su ba. Duk inda masu laifi suke gwamnati ta san shi kuma ta san na san shi amma ta kasa tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.”
PDP, APC Da Sauran Jam’iyyu Duk Abu Daya Ne
Shi ma wani daga cikin wanda suka halarci shirin, ya ce yana da kyau matasa su kiyaye su san wanda za su zaba don jagoranta al’amuran matasa.
Dole Ne A Yi Yakin Neman Zabe Da Tsaro
Abdul kuwa a nasa jawabin, cewa ya yi dole ne sai an yi yakin neman zabe da matsalar rashin tsaro, saboda duba da abubuwan da suka faru sannan ga yanayin da wasu yankuna na kasar ke ciki, dole ne a bai wa dan siyasar da zai iya kawo mafita game da matsalar tsaro dama don dawowa kan turba da gujewa komawa gidan jiya.
Da yake yin dauraya game da shirin, Dakta Getso, ya bayyana cewar akwai bukatar a yi duba na tsanaki wajen zaben dan takara don gujewa cizon yatsa.