• English
  • Business News
Sunday, July 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Tinubu Ya Aika Tawaga Zuwa Jihar Neja Kan Ambaliya Ruwa

by Abubakar Sulaiman
1 month ago
in Manyan Labarai
0
Shugaba Tinubu Ya Aika Tawaga Zuwa Jihar Neja Kan Ambaliya Ruwa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da tawagar gwamnatin tarayya zuwa jihar Neja domin jajanta wa gwamnatin jihar da al’ummar Mokwa bisa mummunar ambaliya da ta hallaka mutane fiye da 151 tare da raba sama da mutum 3,000 da muhallansu.

Tawagar ta haɗa da Ministan Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a, Mohammed Idris, da Ministan harkokin Jin ƙai Farfesa Nentawe Yilwatda.

  • Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sanadin Ambaliya A Neja Ya Karu Zuwa 115
  • Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Rage Farashin Mai Da Iskar Gas

Minista Idris ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya damu matuƙa da iftila’in da ya auku, inda ya umarci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ta tura kayan agaji da taimako cikin gaggawa. Ya kuma bayyana cewa ana shirin ƙara fadada wayar da kan jama’a musamman ga waɗanda ke zaune a yankunan da ake fama da ambaliya.

A nasa jawabin, Farfesa Yilwatda ya ce gwamnatin tarayya ta umurci Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira da wadanda Aka Raba da Gidajensu da ta ci gaba da ba da tallafi ga waɗanda lamarin ya rutsa da su, bayan NEMA ta kammala aikinta na farko. Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakan sake gina manyan hanyoyi da gine-ginen da ambaliya ta lalata.

Mataimakin Gwamnan Neja, Kwamared Yakubu Garba, ya gode wa shugaban ƙasa bisa wannan saurin kai agaji da nuna kulawa. Ya bayyana cewa gidaje 264 da gidajen iyali 503 sun rushe, yayin da gada uku da hanyoyin cikin gari suka lalace gaba daya, lamarin da ya jefa Mokwa cikin matsanancin hali.

Labarai Masu Nasaba

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu

Shettima Ya Ziyarci Buhari A Landan Cikin Sirri Don Duba Lafiyarsa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmbaliyaNeja
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi

Next Post

Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno

Related

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu
Manyan Labarai

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu

11 hours ago
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Labarai

Shettima Ya Ziyarci Buhari A Landan Cikin Sirri Don Duba Lafiyarsa

12 hours ago
Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa
Kotu Da Ɗansanda

Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa

14 hours ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Manyan Labarai

Lauyoyin Natasha Sun Buƙaci Ta Koma Majalisa Ranar Talata Bayan Miƙa Takardun Hukuncin Kotu

14 hours ago
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba

1 day ago
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
Manyan Labarai

Shugabannin Jam’iyyar ADC Na Jihohi 36 Da Abuja Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga David Mark

1 day ago
Next Post
Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno

Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno

LABARAI MASU NASABA

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

July 12, 2025
Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

July 12, 2025
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

July 12, 2025
Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

July 12, 2025
Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

July 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

July 12, 2025
Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

July 12, 2025
Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista

Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista

July 12, 2025
Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi

Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi

July 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.