Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da muhimmin umarnin bayar da fifiko ga aikin ceton rayuka, ba tare da yin kasa a gwiwa ba, domin rage asarar rayuka, sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar, a yau Litinin.
Hukumomi a yankin sun ce mutane 21 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar iftila’in.
Lardin ta aike da sama da ma’aikatan ceto 600, kuma 300 sun riga sun isa wurin da iftila’in ya auku domin shiga aikin ceto da gyara tituna da tura jirage marasa matuka domin tantance asarar da girgizar ta haifar. Haka kuma karin jami’an ceto na kan hanyarsu ta zuwa wurin. (Fa’iza Mustapha)