Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fayyace muhimmiyar matsayar Sin dangane da batun Taiwan, yayin zantawarsa ta wayar tarho da shugaban Amurka Donald Trump a jiya Litinin.
Shugaba Xi, ya jaddada cewa dawowar yankin Taiwan karkashin ikon kasar Sin muhimmin bangare ne na odar kasa da kasa da aka cimma bayan yakin duniya na biyu. Kuma Sin da Amurka sun yi yaki kafada-da-kafada da matakin danniya da na nuna karfin soji, a yanzu kuma kamata ya yi su hada karfi waje guda domin kare nasarar yakin duniya na biyu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, dangantakar Sin da Amurka na gudana bisa daidaito, kuma cikin kyakkyawan yanayi tun bayan taron birnin Busan, don haka ya dace kasashen biyu su wanzar da wannan ci gaba, tare da kara dorawa inda aka tsaya kan turba ta gari, bisa salon daidaito, da mutunta juna da cimma moriyar juna, da fadada sassan hadin gwiwa da rage jerin matsaloli, ta yadda za a kara samun ci gaba, da bude sabbin babukan hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, da samar da karin alherai ga al’ummun kasashen biyu da ma duniya baki daya.
A nasa tsokaci kuwa, Trump ya bayyana shugaba Xi a matsayin shugaba mai martaba. Ya kuma ce ya gamsu da tattaunawar da suka yi a Busan, kana ya amince da batutuwan da shugaba Xi ya tabo dangane da alakar Sin da Amurka. Ya ce kasashen biyu na aiwatar da matakan da suka amince da su yayin taron Busan, kuma kasar Sin muhimmin bangare ne na nasarorin da aka cimma yayin yakin duniya na biyu, kana Amurka ta fahimci muhimmancin batun yankin Taiwan ga kasar ta Sin.(Saminu Alhassan)














