Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon jaje ga shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera, da na Mozambique Filipe Nyusi, bisa ta’adin da mahaukaciyar guguwa ta yiwa kasashen biyu.
Cikin sakon da ya aike ga shugabannin kasashen 2 a ranar Litinin, shugaba Xi ya bayyana matukar kaduwa, da jin labarin yadda guguwar mai lakabin “Freddy”, ta sabbaba rasa rayukan jama’a, da lalata gine-gine a Malawi da Mozambique.
Ya ce “A madadin gwamnatin kasar Sin, da daukacin al’ummar kasar, ina mika sakon ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukan su a wannan ibtila’i, ina kuma gabatar da jaje ga iyalan da suka rasa ‘yan uwan su, da wadanda suka jikkata”.
Kaza lika shugaban na Sin ya yi imanin cewa, kasashen 2 za su farfado daga wannan ibtila’i, kana za su sake gina abubuwan da guguwar ta lalata yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)