A jiya Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga zauren taron Kafafen Yada Labarai da Kwararru na kasashe masu tasowa a duk fadin duniya.
Shugaban ya nunar da cewa, yanzu haka kasashe masu tasowa na dada samun ci gaba cikin wani sabon kwanji da kuma kara taka muhimmiyar rawa a bangaren ciyar da dan Adam gaba.
- Rundunar Sojin Saman Kasar Sin Na Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwa
- ‘Yan Bindiga 3 Da Mai Yin Safarar Makamai Sun Shiga Hannu A Taraba
Xi ya kuma bayyana cewa, kasar Sin a ko yaushe ta kasance ’yar gida a kasashe masu tasowa, kuma za ta ci gaba da kasancewa tare da kasashen.
Har ila yau, a cikin sakon, shugaban ya ce, kasar Sin tana da muradin aiki tare da kasashe masu tasowa a duniya, domin cudanya da mabambantan kasashe cikin gaskiya, da ci gaba da yekuwar samun duniya mai daidaito da ta hada kasashe daban-daban cikin tsari, tare da cin gajiyar tattalin arziki mai gamewa ta hanyar hada karfi da karfe, wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
Shugaba Xi ya yi fatan cewa mahalarta taron za su yi tattaunawa mai zurfi da cimma matsaya da kuma hada hannu wajen kara daukaka matsayin kasashe masu tasowa wajen fada-a-ji yayin da suke nuna wa duniya irin dukufar da suke yi.
A jiya Litinin ne dai aka bude zauren taron Kafafen Yada Labarai da Kwararru na kasashe masu tasowa a duniya a birnin Sao Paulo na kasar Brazil mai taken “Bunkasa da kuma Murmurewa: A Matsayin Sabuwar Tafiya Ga Kasashe Masu Tasowa”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)