Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Angola João Lourenço, bisa lashe zaben shugabancin kasar sa da ya yi.
A cikin sakon na sa, Xi ya ce a shekarun baya-bayan nan, alakar Sin da Angola na kara bunkasa yadda ya kamata, inda sassan biyu ke kara amincewa juna a siyasance, da zurfafa hadin gwiwar su bisa tsari, wanda hakan ke amfanar al’ummun su.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, yana dora muhimmacin gaske, ga ci gaban dangantakar kasar sa da Angola, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Lourenço, wajen daga matsayin kawancen sassan 2 zuwa wani sabon matsayi. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp