Shugaba Bola Tinubu zai yi tafiya zuwa Faransa a gobe Litinin, 19 ga watan Agusta, inda zai bar Abuja, kamar yadda wata gajeriyar sanarwa da Ajuri Ngelale, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar ta tabbatar.
Sanarwar, wacce aka fitar a yau Lahadi, bata bayyana cikakken dalilin tafiyar ba ko tsawon lokacin da zai shafe a can.
- Akwai Raɗaɗi Da Zafi Kan Cire Tallafin Man Fetur Amma Ya Zama Dole – Tinubu Ga masu Zanga-zangar
- Manoma Sun Nemi Tinubu Ya Kara Yawan Tallafin Noma
Duk da cewa ba a bayyana dalilin ziyarar Shugaban ba, mai magana da yawunsa ya tabbatar da cewa Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala gajeriyar ziyarar aiki a Faransa.
Ana sa ran ƙarin bayanai game da tafiyar zai biyo baya daga bisani.