Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da ‘Ogan Boye,’ ya naɗa mutane 60 a matsayin hadimai domin taimakasa masa wajen inganta ayyukan gwamnati da ci gaban al’umma.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 6 ga watan Janairu, 2025, da Sakataran Ƙaramar Hukumar, Ado Muhd Hotoro, ya sanya wa hannu, an bayyana naɗin, wanda ya haɗa da masu kawo rahoto na musamman 18 da za su sa ido kan ma’aikatu, kasuwanni, da cibiyoyin kiwon lafiya.
- Cece-kuce Kan Badaƙalar Kuɗaɗe A NNPCL: SERAP Ta Bukaci Mele Kyari Ya Yi Bayani
- ‘Yan Bindiga Sun Yanka Wa Mutanen Zamfara Haraji Mai Yawa
Wasu muƙaman sun haɗa da Mataimaka na Musamman, Ma’aikatan Tsare-Tsare, da Shugabannin Daraktoci takwas.
Shugaban ya bayyana cewa wannan naɗi na da nufin inganta ayyuka da tabbatar da cewa an samu wakilcin al’umma a mulkinsa.
Ya ƙara da cewa waɗannan hadimai za su taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin da ake fuskanta tare da inganta rayuwar al’umma.
Ya ce an yi naɗin ne bisa cancanta da sadaukarwa, inda ya jaddada cewa dole ne sabbin hadiman su yi aiki tuƙuru domin tallafa wa manufofin ci gaban ƙaramar hukumar.