Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukuyum a Jihar Zamfara, Abubakar Umar Faru, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta bai wa jami’an tsaro makamai na zamani domin ƙaddamar da cikakken farmaki a kan ƴan bindiga da ke ɓoye a Gandun Dajin Gando.
A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Faru ya bayyana cewa ya mika cikakkun bayanan wuraren da ƴan bindigar ke fakewa jami’an tsaro, amma ya ce rashin manyan kayan yaƙi na hana su shiga dajin domin kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya.
- Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Sabon Tsarin Ci Gaban Zamfara Na Shekaru 10
- Uwargidan Shugaban Kasa Ta Bai Wa Nakasassu 250 Tallafi A Zamfara
Ya ƙara da cewa Gandun Dajin Gando ya zama babbar mafakar ƴan bindiga, musamman bayan wasu daga cikinsu da suka yi sulhu a sassan Katsina da Birnin Gwari a Jihar Kaduna sun koma Zamfara. A cewarsa, wannan sauyin wuri ya ƙara tsananta matsalar tsaro a yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yabawa ƙoƙarin jami’an tsaro da ke yankin, amma ya jaddada cewa sai an kai farmaki kai tsaye cikin daji kafin a iya murƙushe ƴan bindigar. Ya kuma zargi ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da gazawa wajen amfani da matsayinsa domin kawo ƙarshen matsalar, duk da kasancewarsa ɗan asalin Zamfara.
Faru ya ce gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi na ƙoƙari gwargwadon ikon da kundin tsarin mulki ya ba su, amma ya bayyana cewa ikon bayar da umarni ga jami’an tsaro na hannun gwamnatin tarayya ne. Gandun Dajin Gando, wanda a baya ake amfani da shi wajen noma da kiwo, ya zama cibiyar ƴan bindiga, lamarin da ya haddasa ƙaura da durƙushewar harkokin noma a Zamfara.














