Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya tsallake rijiya da baya dangane da bukatar tsige shi da aka yi saboda zargin rufa-rufar da ya yi lokacin da barayi suka saci makudan kudade a gonarsa.
Bayan zazzafar mahawara a Majalisar Dokokin kasar, ‘yan majalisa daga jam’iyyarsa ta ANC sun samu rinjaye da kuri’u 214 domin kare shugaban, yayin da masu bukatar tsige shi suka samu kuri’u 148.
- Kasan Wadanda Suka Kawo Boko Haram, Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Atiku
- Qatar 2022: Argentina Ta Je Matakin Wasan Karshe
Sakamakon wannan kuri’a, shugaban majalisar dokoki Nosiviwe Mapisa-Ngakula, ya ce ba za a ci gaba da bukatar tsige shugaba Ramaphosa ba, saboda masu rinjaye sun ki amincewa da bukatar haka.
Wannan ba karamar nasara ba ce da shugaba Ramaphosa wanda ke daya daga cikin shugabannin ANC da suka taka rawa wajen samun ‘yanci da kuma gina dimokuradiyyar Afirka ta Kudu ta samu.
Ramaphosa ya gaji shugaba Jacob Zuma a karagar mulki, bayan da aka tilasta masa sauka daga karagar mulki saboda zargin cin hanci da kuma almundahana da dukiyar kasa.
Tunda Kasar Afirka ta Kudu ta koma tafarkin dimokuradiyya, shugaba Nelson Mandela kadai ya kammala wa’adin mulkinsa ba tare da matsala ba, ganin yadda aka kawar da shugaba Thabo Mbeki da ya gaje shi da kuma Jacob Zuma da biyo baya.