Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo(DRC) Felix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 24 zuwa 29 ga wata, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa.
Da take amsa tambaya game da ziyarar a gun taron manema labarai da aka gudanar a yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta ce, wannan ziyara za ta sanya wani sabon kuzari wajen raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Congo din, da sa kaimi ga ci gaba da samun sabbin sakamako a hadin gwiwar sada zumunta tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp