Shugaban ƙasar Saliyo kuma shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio, ya aike da saƙon ta’aziyya ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da al’ummar Nijeriya da kuma iyalan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa daga birnin Freetown a ranar Litinin, Bio ya bayyana Buhari a matsayin “fitaccen dattijo” tare da yabawa irin gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a yankin Yammacin Afirka a lokacin da yake shugaban ECOWAS.
- Na Yi Rashin Jagora, Buhari Ne Ya Ƙarfafa Min Guiwa Na Yi Takarar Gwamna A Kaduna — El-Rufai
- Rasuwar Buhari: Na Yi Rashin Ɗan’uwa, Aboki, Ɗan Ƙasa Nagari —Babangida
“Mun girgiza kwarai da rasuwar abokinmu kuma tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari. Sadaukarwarsa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Afirka za su daɗe ana tunawa da su,” cewar Bio.
Bio ya tabbatar da goyan bayan ƙasar Saliyo ga Nijeriya a wannan lokaci na alhini, inda ya bayyana cewa ECOWAS da duniya gaba ɗaya sun yi rashi mai girma: “Mun rasa ɗan ƙasa na gari kuma jajirtaccen shugaba.” cewar Julius Bio.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp