Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki, ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya, a yayin ziyararsa a kasar Sin, inda ya gabatar da ra’ayinsa game da tarkon basussuka da wasu kafofin watsa labarun kasashen yammacin duniya suke yayatawa, inda ya ce kasar Sin ta samar da goyon baya, da gudummawa ga Afirka, ta kuma amince gwamnatocin kasashen Afirka su samu basussuka daga wajenta, don haka ya dace kasashen nahiyar su sauke nauyin dake wuyan su.
Shugaba Afwerki ya ce dalilin da ya sa ake dangantawa kasar Sin batun tarkon basussuka, shi ne shafawa Sin din kashin kaji, da lalace nasarorin da Sin ta samu, ko bata hulda, da hadin gwiwa dake tsakanin Afirka da Sin. Amma a hakika, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, na sa kaimi ne ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka.
Shi ma a nasa bangare, shugaban kasar Congo Kinshasa Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, ya yi tsokaci game da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, a yayin da yake zantawa da wakilin CMG a kwanakin baya, inda ya ce Sin ta zuba jari, ta kuma gudanar da ayyukan more rayuwa da dama a nahiyar Afirka. Kuma idan ba a samu irin wadannan abubuwan more rayuwa ba, ba za a iya samun bunkasuwa a ko wace kasa ba, don haka ana bukatar karin hadin gwiwa a wannan fanni.
Ya ce burin kasashen Afirka shi ne kafa dangantakar abokantaka ta cimma moriyar juna, kuma idan kasar Sin ta zuba jari a Afirka, za ta samu kyakkyawar riba, yayin da ita ma Afirka za ta samu moriya. Musamman yankin ciniki cikin ‘yanci na Afirka da ake ginawa, wanda idan komai ya gudana yadda ya kamata, kasashen Afirka za su kasance kasuwar ciniki mafi girma a duniya, wato kasuwar dake kunshe da mutane fiye da biliyan 2. (Zainab)