Bisa gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa birnin Mascow da yammacin Litinin din nan, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar.
Kafin fara ziyarar wadda zai gudanar zuwa ranar Laraba, an shirya masa bikin maraba da zuwa, a filin jirgin saman kasar ta Rasha.
Yayin ziyarar ta sa, shugaba Xi zai gudanar da zuzzurfar musayar ra’ayoyi, tare da mai masaukin sa shugaba Putin, game da akalar kasashen su, da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya dake jan hankalin su.
An shirya ziyarar ta wannan karo da nufin zurfafa tsare-tsare, da aiwatar da hadin gwiwa na zahiri tsakanin kasashen biyu, tare da shigar da sabon kuzari ga ci gaban dangantakar Sin da Rasha. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp