A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musayar ra’ayi tare da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron a garin Dujiangyan da ke birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.
Shugaba Xi da uwargidansa Peng Liyuan ne suka tarbi shugaba Macron da uwargidansa, bayan isowarsu. Shugaba Xi ya yi bayani game da tarihin tsarin ban ruwa na Dujiangyan da kuma ma’anarsa, inda ya ce tsarin ban ruwa na Dujiangyan mai dadadden tarihi ya kasance irinsa daya tilo da har yanzu ake amfani da shi a fadin duniya, wanda ya kasance daya daga cikin nasarorin dan Adam wajen rayuwa da sauran halittu cikin jituwa. Ya ce tarihin gina tsarin Dujiangyan ya shaida halayyar al’ummar Sinawa ta juriya da jajircewa. Yana mai cewa, al’ummar kasar Faransa ma sun kasance masu juriya, dalili ke nan da ya sa kasashen biyu suke iya fahimtar juna da martaba juna fiye da sauran kasashe.
- Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu
- Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa
Shugaba Macron a nasa bangaren ya yaba da tsarin ban ruwa na Dujiangyan da ni’imarsa. Ya ce, abin burgewa ne ganin tsarin ban ruwa da aka gina sama da shekaru dubu biyu da suka wuce yana aiki har yanzu. Ya ce kasancewar Faransa da kasar Sin kasashe masu dadadden tarihi da al’adu, burin al’ummomin kasashen biyu na neman kyakkyawar rayuwa iri daya ne, kuma hadin gwiwar kasashen biyu na iya tabbatar da ci gaba da wadata tare da samar da alfanu ga al’ummominsu.
A yayin ziyarar, kasashen biyu sun bayar da hadaddiyar sanarwa game da inganta gudanar da harkokin duniya da hadin gwiwar tinkarar sauyin yanayi da sauran matsalolin muhalli, da hadin gwiwar amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, da musaya da hadin gwiwa a fannin aikin gona da samar da abinci, da yanayin da ake ciki a Ukraine da Palasdinu da sauransu. (Lubabatu Lei)














