Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da shehun malami Stelios Virvidakis daga jami’ar Athens na kasar Girka da sauran masanan Girka suka aika masa, inda ya yi murnar kafuwar cibiyar yin koyi da juna tsakanin kasashen Sin da Girka ta fuskar al’adu.
A cikin wasikarsa, Xi ya yi nuni da cewa, yau shekaru fiye da dubu 2 da suka wuce, wayewar kan al’ummun Sinawa da Girka sun haskaka nahiyoyin Asiya da Turai, wadanda suka aza harsashi da ba da muhimmiyar gudummowa wajen ci gaban wayewar kan bil Adama. Yanzu kasashen 2 sun kafa cibiyar, a kokarin kara azama kan yin koyi da juna da yin mu’amala a tsakaninsu ta fuskar al’adu, ci gaban wayewar kan kasa da kasa, lamari ne da ke da ma’ana mai muhimmanci a tarihi.
Xi ya jaddada cewa, ba za a iya sa kaimi kan ci gaban zamantakewar al’ummar kasa, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam ba, sai an kara fahimta mai zurfi kan mafarin mabambantan wayewar kai masu dogon tarihi da abubuwan dake kunshe a cikinsu, ta yadda za a yi amfani da kyawawan abubuwan da ke cikin wayewar kan wajen kawo wa ‘yan Adam alheri.
A kwanakin baya ne, shehun malami Stelios Virvidakis daga jami’ar Athens na kasar Girka da sauran masana 5 na Girka, suka aikawa shugaba Xi Jinping wasika tare, inda suka bayyana amincewarsu kan tunanin Xi Jinping dangane da wayewar kai, tare da yin karin bayani kan yadda aka shirya kafa cibiyar yin koyi da juna tsakanin kasashen Sin da Girka ta fuskar al’adu da kuma shirin raya cibiyar. (Tasallah Yuan)