• English
  • Business News
Thursday, September 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Manyan Shugabannin Kasar Saudiyya Da Kuma Gana Da Shugabannin Wasu Kasashen Larabawa Bi da Bi

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Manyan Shugabannin Kasar Saudiyya Da Kuma Gana Da Shugabannin Wasu Kasashen Larabawa Bi da Bi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sarkin masarautar Saudiyya, Salman bin Abdul Aziz Al Saud a fadarsa dake birnin Riyadh a ran 8 ga wata da yamma, agogon wuri.

Xi ya ce, kasarsa ta mayar da Saudiyya a matsayin wata muhimmiyar kasa dake taka rawar gani a harkokin duniya, inda take fatan kara mu’amalar manyan tsare-tsare tare da Saudiyya, da zurfafa hadin-gwiwa a bangarori daban-daban, a wani kokari na kiyaye moriyarsu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

  • Rashin Tsoma Baki Ya Sa Kasar Sin Ke Samun Karin Abokai

A nasa bangaren, sarki Salman ya yi marhabin lale da zuwan shugaba Xi, inda a cewarsa, yana matukar maida hankali kan raya dangantaka tare da kasar Sin, da kuma bayyana fatansa na samar da ci gaban huldodin kasashen biyu, bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni.

Shugabannin biyu sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar kulla dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni, tsakanin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da kasar Saudiyya, inda suka amince cewa, za su gana a kasashensu a kowace shekara.

A dai wannan rana, shugaba Xi ya yi shawarwari tare da yariman masarautar Saudiyya, kana firaministan kasar Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud, inda suka yarda cewa, za su daga matsayin shugabancin kwamitin hadin-gwiwar manyan jami’an kasashen biyu, zuwa matsayin firaminista.

Labarai Masu Nasaba

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

Shugabannin biyu sun kuma halarci bikin mika wa juna takardun yarjeniyoyin hadin-gwiwar kasashensu, a fannonin da suka shafi raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da aikin shari’a, da ilimi, da makamashin hydrogen, da zuba jari, da gidajen kwana da sauransu.

Bayan shawarwarin, shugaba Xi ya halarci bikin maraba da yariman Muhammad ya shirya masa, a madadin sarkin Salman bin Abdul Aziz Al Saud.

Sannan a wannan rana da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kuma gana da takwaransa na kasar Masar, Abdel Fattah al Sisi a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.

Yayin ganawar, Xi ya ce, bisa halin da ake ciki yanzu a duk duniya, da ma shiyyoyi daban-daban na fuskantar manyan sauye-sauye, yana da muhimmanci a raya huldodin Sin da Masar bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoi. Ya ce ya dace kasashen biyu su yi kokari tare, don neman cimma burin gina al’ummominsu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, ta yadda za’a kara samar da sabon ci gaba, ga dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni.

A nasa bangaren, shugaba Sisi ya ce, ya zo kasar Sin don halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka yi a watan Fabrairun bana a Beijing, inda ya yi shawarwari masu gamsarwa tare da shugaba Xi. Ya ce, ya ziyarci kasar Sin a wancan lokacin ne don goyon bayan kasar, da karfafa dangantaka tare da kasar. Sisi yana da yakinin cewa, a sabon wa’adin aikin shugaba Xi, dangantakar kasashen biyu za ta samu karin ci gaba, kana, kwalliya za ta biya kudin sabulu, wajen karfafa hadin-gwiwarsu a bangaren shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Bugu da kari, da safiyar yau 9 ga wata ne, bi da bi shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasar Tunisiya Kais Saied da na kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani da na kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh da na kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da na Comoros Azali Assoumani da firaministan kasar Iraki Mohammed Shia al-Sudani da sarki Tamim Bin Hamad Al Thani na masarautar Qatar a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya. (Murtala Zhang, Ibrahim Yaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Li Keqiang Ya Halarci Taron Tattaunawa Tare Da Shugabannin Manyan Hukumomin Tattalin Arzkin Duniya

Next Post

Gasar Cin Kofin Duniya: Croatia Ta Kora Brazil Gida

Related

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar
Daga Birnin Sin

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

16 minutes ago
Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 
Daga Birnin Sin

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

18 hours ago
Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
Daga Birnin Sin

Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 

19 hours ago
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Daga Birnin Sin

Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba

20 hours ago
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
Daga Birnin Sin

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban

21 hours ago
An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
Daga Birnin Sin

An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 

22 hours ago
Next Post
Gasar Cin Kofin Duniya: Croatia Ta Kora Brazil Gida

Gasar Cin Kofin Duniya: Croatia Ta Kora Brazil Gida

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

September 18, 2025
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

September 18, 2025
Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na Taimaka Ga Bunkasa Al’adunta Da Mu’amalar Al’adu Tsakaninta Da Kasashen Duniya

Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na Taimaka Ga Bunkasa Al’adunta Da Mu’amalar Al’adu Tsakaninta Da Kasashen Duniya

September 18, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Kama Sojan Gona Da Motocin Sata 3 A Jigawa

September 18, 2025
Yadda Muka Zama Bayin ‘Yan Bindiga -Mazaunin Wani Kauye

’Yan Bindiga Sun Sako Ma’aurata A Katsina Bayan Karɓar N50m A Matsayin Kuɗin Fansa

September 18, 2025
Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis

Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis

September 18, 2025
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

September 18, 2025
’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja

’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja

September 18, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB

September 18, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

September 17, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.