• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Cuba

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Da safiyar yau Jumma’a 25 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Cuba Miguel Diaz-Canel, wanda shi ne sakatare na farko na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Cuba, wanda kuma a yanzu haka yake ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. 

A yayin shawarwarin, Xi ya ce, kasar Cuba, ita ce kasa ta farko da ta kulla huldar diplomasiyya a tsakaninta da jamhuriyar jama’ar kasar Sin a bangaren yammacin duniya. Kuma huldar da ke tsakanin Sin da Cuba, ta zama abun misali a fannin hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen gurguzu, da kuma taimakawa juna a tsakanin kasashe masu tasowa cikin sahihanci.

  • Shugaban Zimbabwe Ya Yi Tsokaci Game Da Sabon Ginin Majalissar Dokoki Da Kasar Sin Ta Samar Da Kudaden Gudanarwa

Ya ce kasar Sin na son kara zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa a tsakaninta da Cuba, da habaka hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin kasashen 2, da mara wa juna baya kan batutuwan da suke shafar babbar moriyar juna, da taimakawa juna a al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da raya kasa ta gurguzu mai halin musamman kafada da kafada, da kuma zurfafa huldar da ke yi tsakanin Sin da Cuba a sabon zamani.

A nasa bangaren, Miguel Diaz-Canel ya ce, ziyararsa ta nuna yadda Cuba ke dora muhimmanci kan raya huldar hadin gwiwa a tsakaninta da Sin.

Kaza lika Cuba ta amince da yadda kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karkashin shugabancin Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar, ya ba da gudummowa a tunani da aiki, a fannin raya kasar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin a sabon zamani, lamarin da a ganin Cuba, ya karfafa gwiwar dukkan sassan duniya masu kokarin samun ci gaba sosai. (Tasallah Yuan)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Kofin Duniya: Iran Ta Lallasa Wales Da Ci 2

Kofin Duniya: Iran Ta Lallasa Wales Da Ci 2

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.