Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ce sabon ginin majalissar dokokin kasarsa da Sin ta tallafa da kudaden aiwatar da shi, na daf da kammala kafin mika shi ga Zimbabwe.
Shugaba Mnangagwa ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a harabar ginin, ya kuma yi amfani da damar wajen fayyace ajandar majalissar dokokin kasar, cikin ’yan watannin da suka rage, kafin babban zaben kasar na tsakiyar shekara mai zuwa.
Cikin jawabin nasa shugaban ya jinjinawa kasar Sin, bisa makudan kudaden da ta samar domin gudanar da ginin majalissar dokokin kasar a yankin Mt. Hampden, mai nisan kilomita kusan 25 daga arewa maso yammacin birnin Harare, fadar mulkin kasar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp