Jagoran gwamnatin sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, ya ce a cikin wannan mako zai bayyana wa al’ummar kasar jadawali dangane da yadda za a gudanar da zabuka da kuma mika mulki ga fararar hula.
Janar Abdourahman Tiani, wanda ya bayyana haka yayin gabatar da jawabi game da zagayowar ranar Jamhuriyar, ya yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar matakan da kungiyar ECOWAS ta dauka kan Nijar.
- Kwamitin Tsaron MDD Ya Kada Kuri’a Kan Tsagaita Wuta A Gaza
- Sanata Barau Jabril Na Kokarin Hana Shoprite Tashi Daga Kano
A hannu guda kuma, ya bayyana alfahari da matakin da suka dauka na soke wasu yarjejeniya da ke tsakanin Nijar da Faransa.
A ranar Juma’ar da ta gabata kungiyar Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), ta amince da cewar an yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, bayan tabbatar da hakan a hukumance ne kuma ECOWAS ta dakatar da kasar daga cikinta har sai lokacin da aka mayar da kundin tsarin mulki.
Takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar dai na ci gaba da yin tasiri a bangarori da dama, musamman akan harkokin kasuwanci inda dubban ‘yan kasuwa a ciki da makwabtan kasar suka tafka asarar kayayyakinsu da suka makale akan iyaka.
Wannan dai na zuwa sakamakon matakin ladaftarwar da hukumomin kasa da kasa suka dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.