Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da sashen farko na layin dogo irin na zamani a jihar Legas dake kudu maso yammcin kasar.
Shugaba Tinubu ya kaddamar da layin dogon ne a jiya Alhamis, wanda ya ce ya bude sabon babi na shawo kan kalubalen cinkoson ababen hawa, da jinkirin zirga zirga da ake fuskanta a jihar mai dunbin hada hadar kasuwanci.
- Xi Ya Jaddada Bukatar Raya Sabon Makamashi Mai Inganci A Kasar Sin
- GDPn Kasar Sin Na Shekarar 2023 Ya Karu Da Kashi 5.2 Cikin Dari
Kamfanin CCECC na kasar Sin ne dai ya aiwatar da ginin layin dogon, wanda aka fara tun a shekarar 2021. Layin mai lakabin LRMT “Red Line”, na da tsawon kilomita 26.5, da kuma tashoshi 8.
Da yake jawabi yayin kaddamar da layin dogon a Ikeja, fadar mulkin jihar ta Legas, Tinubu ya ce aikin wani mafarki ne da ya zamo gaskiya, kuma nasara ce da aka cimma bayan gwamnatocin baya sun shafe shekaru da dama suna aiki tukuru.
Shugaban na Najeriya, wanda daga bisani ya hau jirgin kasan, ya kuma ganewa idanun sa bikin sanya hannu kan takardun amincewa da fara gina sashe na 2 na layin dogon na LRMT Red Line, tsakanin hukumar sufuri ta birnin Legas da kamfanin CCECC. (Mai fassara: Saminu Alhassan)