Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya bayyana cewa shugaban kasan Nijeriya da zai gaji Muhammadu Buhari bayan karewar wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu na shekara mai zuwa, zai kashe kudaden harajin da Nijeriya za ta samu a wajen biyan bashi ne har zuwa shekarar 2026.
A halin yanzu dai, gwamnatin tarayya tana kashe kusan kaso 80 kan biyan bashi kadai, wanda ta bai wa ayyukan ci gaba na tsakanin kaso 15 zuwa 20.
Illar dai ita ce, kowani kobo 100 da aka samu, kasa da kobo 20 ne kadai ake tafiyartar da su wajen cika alkawarin da aka dauka lokacin yakin neman zabe.
A haka kuma, gwamnatin tarayya tana shirin kara kinkimo wa Nijeriya bashin kari da na naira tiriliyan 46.63 kafin karshen shekarar 2022.
“Duk da karancin samun kudaden shiga, wanda akwai bukatar samar da ababen more rayuwa a Nijeriya. Yana da matukar muhimmanci a samu daidaituwar tattalin arziki a Nijeriya tare da samun kayayyakin more rayuwa da za su inganta harkokin al’umma,” in ji Mista Ari Aisen.
Ya kara da cewa Nijeriya a matsayinta na mai fitar da arzikin man fetur ta kasa samun alfanun karuwar farashin man fetur a duniya wajen samar da ayyukan ci gaba kasa, sakamakon makudan kudaden da take kashewa wajen biyan tallafi a bangaren man fetur.
IMF ya gargadi gwamnatin tarayya da ta gudanar da daukan matakin gaggawa wajen karuwar samar da kudaden shiga, idan kuma ba haka ba za ta ci gaba da biyan bashi har zuwa shekarar 2026.
Asusun ya ci gaba da bayyana cewa, bisa turbar da Nijeriya take a halin yanzu na tattalin arziki, kudaden ruwa na bashi za su lakume gaba daya kudaden shigan Nijeriya na tsawan shekaru hudu.
Wakilin IMF a Nijeriya, Mista Ari Aisen ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da rahoto kan tattalin arzikin yankin Afirka wanda ya gudana a Abuja.
Gwamnatin tarayya za ta kashe naira tiriliyan 3.61 wajen bayan bashi a cikin kasafin kudin Nijeriya na shekarar 2022.
Naira tiriliyan 3.61 da aka amfani da shi wajen biyan bashi shi ne kashi 34 na adadin yawan kudaden haraji da ake tsammanin gwamnatin tarayya za ta samu a 2022.
Nijeriya ta tsinci kanta a cikin mummunan bashi wanda ya kai na naira tiriliyan 45, yayin da ofishin kula da basuka ke kara shirin amso bashi na naira tiriliyan 6.39 domin a cike cibin kashafin kudi na shekarar 2022.
Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tana fuskantar matsinlamba kan karuwar yawan basukan da ake bin kasar nan.