A bisa qoqarin sayar da hannun jari da kuma qara bunkasa ayyukan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Kasar nan, Shugaban Hukumar Dakta Abubakar Dantsoho, ya kai ziyarar aiki domin yin gangami neman masu zuba hannun jari a tashoshin Jirgin ruwa na Onne da ta jihar Ribas.
Ya kai wannan ziyarra ce, biyo bayan wadda ya kai a tashoshin Jiragen ruwa na Apapa da ta Tin-Can da ke a jihar Legas a ranar 27 ga watan Nuwambar 2024.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
- Hukumar NPA Ta Ƙara Kaimi Wajen Janyo Masu Zuba Hannun Jari
Gwamnati dai ta mayar da hankali wajen ganin ta tabbar da sanya ido wajen kula da ayyukan tashoshin Jiragen ruwa na qasa, duba da yawan a’lummar qasar da suka kai sama da miliyan 200.
Kazalika, ya kuma kai wata ziyara zuwa ga kafanin mai na BRAWAL Oil Services Ltd, tashar Onne Multipurpose Terminal, INTELS, INDORAMA, West African Container Terminal (WACT), NOTORE, da kuma ta Ribas.
A lokacin ziyarar ya jaddada mahimmancin zuba jari a fannin, musamman a Afirka ta Yamma da Afika ta Tsakiya.
Ya sanar da cewar hukumarsa za ta iya yin aiki kafada da kafada ne kawai, tare da yin gasa, ta hanyar masu zuba hannun jari a fannin, matukar an samar da kayan aikin da suka dace.
Dantsoho ta sanar da cewa, Hukumar za ta mayar da hankali duba da nauyin da ministan da ke kula da albarkatun cikin ruwa da tattalin arziki Adegboyega Oyetola, na cewar, Hukumar ta tabbatar da qara yawan samo masu son zuba hannun jari a fannin.