A wata hira da wakiliyar CMG, shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya yi nuni da cewa, tun daga farkon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na farko a shekarar 2017 zuwa dandalin tattaunawar na biyu, sannan kuma ya zuwa yau, yanayin duniya ya canja. Musamman, yadda cutar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin ko wace kasa.
A sa’i daya kuma, a yayin da ake fuskantar kalubalen sauyin yanayi, ya zama wajibi a bunkasa tattalin arzikin maras gurbata muhalli. Bugu da kari, kasashe masu karamin karfi da masu matsakaitan kudin shiga, su ma suna fuskantar matsin bashi, alal misali kasar Sri Lanka na fama da matsalar basussuka.
Yana mai cewa, a yayin da duniya ke fama da sabbin matsaloli da manyan kalubaloli, muna fatan samun mafita ta hanyar shiga cikin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya. (Ibrahim)