Kun taba yi wa kanku wadannan tambayoyin: Idan kuna da yaran kanti, kun taba zama ku da su kun yi yarjejenya kafin su fara aiki, ma’ana matsyinsa a wannan kantin? Idan kun yi haka kun rubuta? Idan ba ku yi ba, kuna ganin ba shi da amfani shi ya sa ba ku yi ba?
Idan kai yaran kanti ne, tsakaninka da Allah kana taimaka wa maigidanka ya cimma nasarar kasuwancinsa, ko kuwa kana zuwa ne kawai don kar a ce ba kada sana’a, ko kuwa kawai maneji kake yi idan ka samu wani gurinza kai tafiyarka ka barshi, duk da taimakonka da ya yi, don kai maka samu naka?
- Bukatar ‘Yan Siyasa Su San Kalaman Da Za Su Furta Lokacin Kamfen
- Ya Yi Yunkurin Jefa Matarsa Rijiya Don Zargin Tana Cutarsa
Makasudin yin wadannan tambayoyi shi ne tunatar da ‘yan kasuwa game da wani mahimmina l’amari game da harkokin kasuwancinsu na yin ka’ida ko na ce gina kasuwanci akan doron gaskiya inda dan kasuwa zai kubuta daga duk wani abu wanda zai iya zamar masa tarnaki a kasuwancinsa.
Dalilin yin wadancan tambayoyi ba komai bane illa na zaburar da ‘yan kasuwa da su masu taimaka musu, su tsaya akan abin da sukayi alkawari a kansa inda ko wane bangare zai gamsu ya yi abin da yarjejeniya ta bashi damar yi.
Jama’a da yawa su kan yi min tambaya akan wannan batu na tsakanin yaron kanti da maigidansa.
Yawancin wadanda suke yi min wadannan tambayoyi sun tunasar da ni a kan yadda halin yaran kantin yake, ma’ana yawancinsu ba su da gaskiya, burinsu kawai shi ne su sami abind a za su samu su yi gaba.
Wasunsu kuma ko da an yi wannan yarjejeniyar sai ka ga sun sa ido da abin da kai maigidansa ake samu inda za’a ga burinsu kawai su ga sun cuci masu gidansu. Wadannan su ne kadan daga cikin abin da ‘yan kasuwa da na yi hulda da su suka fada min. Yawancin su kuma daga yaran kanti da na yi musu tambayoyi da binciken da na yi, musamman daga Kano, Legas da sauran jihohin kasar nan sun gayamin irin yadda iyayen gidansu suke azabtar da su da sunan kasuwanci.
Akwai wanda ya ce min shi gaba daya bai san ma men ene aikinsa ba, saboda gaba daya shi ne yake dawainiya da ‘yayan maigidansa, inda ya ce min shi ne kai yaransa makaranta shi ne kai matansa unguwa a mota sannan duk wani abu idan ya taso ko akasuwa ko a gida shi ne. Ya kara da cewa wani abun bakin ciki shi wannan maigidan nasa yana da ‘ya’ya maza samari wadanda sa’aninsa ne amma duk suna zuwa makarantar gaba da sakandare, amma shi da ya ce masa shi ma yanaso ya koma makaranta sai wannan maigidan nasa ya kekasa kasa yace sam ba za ta yiwu ba, ida nya koma makaranta waye zai ci gaba da dawainiyar kai yara makaranta da kai su Hajiya unguwa?
Mun shafe minti tara da sakan 42 muna magana da shi a waya. Ni dai a gaskiya bayan mun gama wannan waya sai na shiga tunani da tambayar kaina wadannan tambayoyi. Shin kuwa shi wannan mutumin yana da imani? Sannan kuma shin kuwa yana kaunar wannan yaron tun da kiri-kiri ya hana shi tafiya makaranta, sannanna kuma tambayar kaina cewa, wai ma shin gaske ne duk abin da wannan yaron ya fada min a waya?
Saboda ni a gani na ba zan gasgata abin da ya ce min ba ko na karyata, face na ji daga daya bangaren. Ma’ana na ji ta bakin Alhaji saboda ta haka ne kawai duk wani mutum zai san wace irin shawara zai bayar, tun da shi wannan dan’uwa ya nemi na bashi shawarar yadda zai bullowa al’amarin ga shi kuma sai aka yi rashin sa’a ba gari daya muke ba domin mun yi hannun riga. Allah Ya kyauta.
Shugabanci nigari
Bincike ya nuna kashi 99 cikin 100 a kamfanonin da suke kasashen turai da Asiya kai har da Afirka sun ci nasara ne saboda yadda hulda me kyau take gudana tsakanin ma’aikata da abokan hulda da masu kamfanoni.
Nasara tana samuwa ne in dai su shugabanni ko shi shugaba ya zama abin koyi ga ma’aikatansa. Saboda haka a nan dole shugab ako maigida ya zama;1. Mai gaskiya 2. Mai dattaku 3. Mai cika Alkawari.
Gaskiya: a kasuwanci ita ce kashin bayan ci gaban kasuwancin. Tilas maigida ka zama mai gaskiya idan kana so yaranka su zama masu gaskiya.
Sannan idan Allah ya taimake ka kun yi ka’ida da yaranka za ka rika biyansa hakkinsa, to ka zama mai cika alkawari wajen kiyaye abin da aka yi yarjejeniya a kai. Ka zama mai dattaku: Ka zama mai dattaku don ka zama abin misali ga yaranka kada ka yi masakarya, domin duk sanda yaron kaya fahimce ka kai makaryaci ne ka kade a wurinsa domin da sannu zai maka abin da zai baka mamaki, kuma kar ka yi kuka da kowa sai kanka domin kai ne ka jawo ba ka ja girmanka ba shi ya sa shi kuma ya fahimta har ya cuce ka.
Alkawari: Dole ka cika shi domin ka san alkawari abin tambaya ne ko bayan ka mutu, Allah shi da kansa zai cika alkawarin da ya daukar wa bayinsa, to ka ga ya zama dole a gareka ka cika alkawari.
Halayyarka halayyar ma’aikatanka!
Hali wani abu ne da yake tuka rayuwar mutum zuwa ko ina, kamar direba a cikin mota yadda zai sarrafa ba zai taba yadda ya yi wani abu wanda zai iya sa rayuwarsa cikin hadari ba, ko a ce mutane ya dauko a motar za su nufi wani waje a wannan motar, saboda haka duk wadanda aka dauko a motar nan kowa zai dauki yardarsa ya ba wa wannan direban saboda burinsu a je lafiya inda aka nufa ba tare da matsala ba. Bissalam.