ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabanci Na Gari Shi Ne Sirrin Zaman Lafiya Da Ci Gaban Kasa

by CMG Hausa
3 years ago
Zaman lafiya

An rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, bayan an sake zaben Xi Jinping a matsayin shugaban kasar Sin a wa’adi na uku, na shekaru 5.

Jawabin da shugaban ya yi a jiya, ya ja hankalina matuka, inda yake cewa, amincewa da shi da jama’a suka yi, ita ce ke ba shi kwarin gwiwar ci gaba da yin aiki, wanda babban nauyi ne da ya rataya a wuyansa.

  • Yankin Daji A Kasar Sin Ya Karu Da Kadada Miliyan 22 Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

Ba shakka, sirrin ci gaban kowacce kasa da ma tabbatuwar zaman lafiya a kasar, shi ne shugabanci na gari. Kuma sai shugaba ya zama nagartacce kafin al’umma su aminta da shi.

ADVERTISEMENT

Jagorantar mutanen da yawansu ya kai biliyan 1.4, ba karamin abu ba ne. Hausawa kan ce idan dambu ya yi yawa, to ba ya jin mai. Sai dai wannan zance ya sha bambam da yanayin kasar Sin, domin an ga yadda al’ummar kasar da ta zarce yawan na kowacce kasa a duniya, ke rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana da wadata, haka kuma sun kasance masu matukar biyayya ga shugabanninsu tare da amincewa da manufofin da suka gabatar.

Karkashin jagorancin Xi Jinping, kasar Sin ta samu muhimman nasarori da ba a taba gani ba a tarihi, lamarin da jagorancin al’ummar kasar shiga wani sabon babi na ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Misali, a karkashin shugabancinsa ne kasar Sin ta yi adabo da talauci baki daya, shekaru 10 kafin ma lokacin da MDD ke fata. Haka kuma, jama’ar kasar na more zaman lafiya da kwanciyar hankali da zaman jituwa tsakanin mabanbantan kabilu dake akwai. An kuma ga yadda kasar Sin da ba ta da yawan filayen noma, take iya ciyar da al’ummarta har ma take bayar da gudunmawar abinci ga masu bukata, baya ga yadda kasar ta kai matsayin koli wajen jagorantar duniya a fannonin fasahohin zamani da tattalin arziki da sauransu.

Shugaban ya kara da cewa, zai sadaukar da kansa, kuma zai yi aiki tukuru bisa bukatun kasa, da muradun jama’a. A ganina, shugaba kasar Sin ya riga ya cika burin al’umma da muradinsu, shi ya sa suka aminta da shi, suke ba shi goyon baya, tare da kara ba shi ragamar mulkin kasar. Ba makawa alkwarin nan da ya yi musu, zai cika shi kamar yadda aka gani a baya.

Hakika sake zabensa da Sinawa suka yi, ya tabbatar da cewa, suna son ci gaba da more rayuwa ta jin dadi da sauran al’ummomin duniya ke muradi. Haka kuma, wannan ya tabbatar wa duniya cewa, salon demokuradiyyar kasar Sin, demokradiyya ce ta al’umma domin al’umma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
Chelsea Za Ta Shirya Wa Musulmi Shan Ruwa A Watan Ramadan 

Chelsea Za Ta Shirya Wa Musulmi Shan Ruwa A Watan Ramadan 

LABARAI MASU NASABA

Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

November 15, 2025
Yadda Za Ku Gyara Kanku

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.