A wani yunkuri na nuna shirinsa da bajintarsa na zama shugaban jam’iyyar APC na kasa, tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci wasu tsoffin gwamnonin APC.
Tsoffin gwamnonin sun hada da Muhammad Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara; Mallam Nasir Elrufa’i, tsohon gwamnan jihar Kaduna; Simon Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato; da Abubakar sani Bello, tsohon gwamnan jihar Neja.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sake nuna cewa, shi dan jam’iyya ne, wanda ke aiki ba dare ba rana don ganin Jam’iyyar APC ta kai ga Nasarori.
A wani zama da shugabannin jam’iyyar APC na jihohin Arewa maso yamma da suka hada da Kaduna, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kebbi da Jigawa suka yi a jihar Kaduna a ranar Litinin 25 ga watan Yulin 2023, sun rattaba hannu kan goyon bayansu ga Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Shugabannin jam’iyyar, sun ce, sun yanke hukuncin goyon bayan Ganduje ne bisa la’akari da rawar da ya taka wurin wayar wa al’ummar Arewa sanin muhimmancin dan takarar da ta tsayar a zaben da ya gabata, wanda hakan ya kai Jam’iyyar ga Nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp