Tsofaffin ‘yan majalisar tarayya 72 sun amince da zaben Sanata Godswill Akpabio da Sanata Jibril Barau a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa a majalisar ta 10.
Amma, wata kungiya da ke biyayya ga wani dan takarar shugaban Majalisar Dattawa mai suna Good Governance Initiative (GGi), ta yi fatali da kudurin Tsofaffin Sanatocin kan matakin da suka dauka, inda ta bayyana kudurin na su a matsayin wulakantawa da rashin bin tsarin dimokuradiyya.
Tsofaffin Sanatocin dai, sun ce an basu shawara ne kan kudurin na su sabida duba da bukatar yin adalci na siyasa kan shugabancin kasa kan shiyyoyi da ake da su a Nijeriya.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, mai kira kuma shugaban kungiyar Sanatoci masu zaman kansu, Sanata Basheer Lado, ya ce tsofaffin ‘yan majalisar na goyon bayan mayar da shugabancin majalisar dattawa zuwa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta siyasa.