Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar da cewa, za a gudanar da taron kolin Sin da Asiya ta Tsakiya daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Mayu a birnin Xi’an dake lardin Shaanxi, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai jagoranci taron.
Kakakin ma’aikatar Hua Chunying, ta sanar da ewa, shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da shugaban Tajikistan Emomali Rahmon, da shugaban Turkmenistan Serdar Berdimuhamedov da kuma shugaban Uzbekistan Shavkat Miromonovich Mirziyoyev, za su hallarci taron bisa gayyatarsu da aka yi musu.
Har ila yau, bisa gayyatar da Shugaba Xi ya yi musu, Shugabannin Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, da shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da shugaban Tajikistan Emomali Rahmon da shugaban Uzbekistan Shavkat Miromonovich Mirziyoyev za su yi ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 16 zuwa 20 ga watan Mayu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, taron kolin Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya, muhimmin taro ne na farko da kasar Sin za ta gudanar a bana, kana shi ne karo na farko da shugabannin kasar Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya da abin ya shafa, za su halarci taron koli kai tsaye a cikin shekaru 31 bayan kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, don haka taron kolin yana da babbar ma’ana a tarihin raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa, za a gudanar da taron kolin Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya tun daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Mayu a birnin Xi’an dake lardin Shaanxi.
Wang Wenbin ya yi bayani da cewa, a yayin taron kolin, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da muhimmin jawabi, sannan shugabannin kasa da kasa masu halartar taron, za su waiwayi tarihin raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya, da musayar ra’ayoyi kan manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna ciki har da tsarin raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya da hadin gwiwarsu da sauransu, kana za su daddale wata muhimmiyar takardar siyasa tare.
Kakakin ya yi imanin cewa, bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, za a tsara taswirar raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya, da kuma bude sabon babi na hadin gwiwarsu baki daya. (Safiyah Ma, Zainab Zhang)