Yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta jagoranci taron manema labarai da aka saba yi. Kwanan baya, an ba da labari cewa, Sin za ta tura wakilinta na musamman mai kula da harkokin yankin Turai da Asiya Li Hui zuwa Rasha, da hedkwatar EU, da Poland, da Ukraine da Jamus da kuma Faransa, inda zai gudanar da ziyarar aiki tun daga ranar 2 ga wata mai zuwa, don gudanar da shawarwari karo na biyu, game da ingiza magance rikicin Ukraine a siyasance.
A yayin taron, ‘yan jarida sun tambayi jami’ar dalilin Sin na tura wakilinta a wannan lokaci. A cewar Mao Ning, yanzu haka shekaru 2 ke nan tun bayan tsanantar rikicin Ukraine a dukkanin fannoni. Har illa yau, ana fama da yaki, matakin da ya sa dole a sanya bukatar farfado da zaman lafiya gaba. Duk matakan da Sin take dauka, buri daya ne tilo, wato kaiwa ga matsaya daya, ta dakatar da yaki, da taka rawar gani wajen gudanar da shawarwari.
- Yaushe Za A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Zirin Gaza?
- Masanin Kasar Zambia: Tattalin Arzikin Sin Ginshike Ne Ga Duniya
Game da kalaman shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron don gane da halin da ake ciki a Ukraine, Mao Ning ta ce, Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban, da su kai ga cimma matsaya daya ta sassauta halin da ake ciki, da ingiza kokarin tsagaita bude wuta, kana Sin za ta ci gaba da taka rawarta a fannin magance rikicin a siyasance.
Yayin da aka tabo batun tekun Nanhai na Sin kuwa, jami’ar ta ce Sin na mai da hankali sosai kan ayyukan sabawa doka da bangaren Philippines ke yi a tekun na Nanhai. Har ila yau, Sin za ta dauki matakan da suka wajaba, don kiyaye cikakken yankunanta, da ikon tekunta, da ma tabbatar da zaman lafiya da karko a tekun. (Amina Xu)