Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi karin haske kan sukar da kwararrun MDD suka yi, game da yadda ake nuna wariyar launin fata a Amurka, a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa Talatar nan.
Ya bayyana cewa, a matsayinta na kasar da ta sanya hannu a yarjejeniyar kasa da kasa kan kawar da duk wani nau’i na nuna wariyar launin fata, Amurka ta dade tana kitsa karairayi da yada jita-jita game da nuna wariyar launin fata a wasu kasashe, a matsayin wani makami na nuna danniya da magudin siyasa, amma duk da haka ba ta taba fuskantar gaskiyar cewa, cutar nuna wariyar laufin fata da ke ci gaba karuwa a kasar ta zama ruwan dare ba.
A wannan karon, mahawarar da kwamitin MDD ya yi ta neman kawar da wariyar launin fata, babu shakka ya sake aikewa da sako mai karfi ga gwamnatin Amurka.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, Amurka tana alfahari da kanta a matsayinta mai kare hakkin dan Adam kan wasu kasashe, amma ba ta san cewa, ta dade tana zama mai take hakkin dan Adam a idon kasashen duniya ba.
A watan Satumba ne, kwamitin MDD mai yaki da nuna wariyar launin fata, zai gabatar da jawabinsa na karshe kan rahoton aiwatar da yarjejeniyar kawar da nuna wariyar launin fata a Amurka, kuma kasar Sin za ta jira ta ga abin da zai biyo baya.(Ibrahim)