A yau, al’ummar kasar Sin sun gudanar da wani gagarumin gangami da faretin soji a birnin Beijing na kasar, domin tunawa da cikar shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Shugabanin wasu kasashe 26 ne suka halarci bikin tunawa da ya gudana, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin cewa, jama’ar kasar Sin za su tsaya tsayin daka wajen bin tafarki na gaskiya, wanda zai haifar da ci gaban daukacin dan Adam, da bin hanyar raya kasa cikin lumana, da yin aiki kafada da kafada da al’ummun kasashe daban daban, wajen gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama.
Me ya sa Sinawa za su iya bin tafarki na gaskiya? Domin sun dade suna jin radadin yake-yake.
- Ya Kamata El-Rufai Ya Yi Bayani Kan Zargin Gwamnati Na Biyan ‘Yan Bindiga Kuɗaɗe – Datti
- Xi Jinping Ya Duba Faretin Rundunonin Sojoji Da Kayayyakin Soja, Shugabannin Kasashe 26 Su Ma Sun Halarci Bikin
Kasar Sin babban fagen daga ne a yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Lokacin da sojojin Japan suka fara mamaye kasar Sin a shekara ta 1931, Sinawa sun kasance na farko a duniya wajen daga tutar yaki da tafarkin murdiya. Yayin da wasu kasashen yammacin duniya ke tunanin magance yaki da ‘yan Nazi, sojoji da fararen hula na kasar Sin sun riga sun tashi haikan don yaki da maharan kasar Japan, ko da yake ba su da makamai masu inganci a lokacin.
Sama da shekaru 80 da suka gabata, kasar Sin ta kasance cikin talauci da rauni, kuma sadaukarwar da Sinawa suka yi wajen kare kasarsu tana da yawa. Bisa kididdigar da aka yi, yawan sojojin kasar Sin da fararen hula na kasar da suka rasa rayuka, ko kuma suka ji rauni a yakin da suka yi da sojojin Japan ya zarce miliyan 35, inda yawan hasarar da aka samu ya haura dala biliyan 600. Al’ummar kasar Sin, bisa babbar sadaukarwar da suka yi, sun samar da damar cin nasara a yakin da jama’ar kasashe daban daban suka yi na kin tafarkin murdiya. Saboda a yayin yakin na tsawon shekaru 14 da Sinawa suka yi da maharan kasar Japan, fagen daga dake kasar Sin ya janyo hankalin kaso 60% zuwa 94% na sojojin kasa na kasar Japan. Wannan yanayi ya wargaza muradin sojojin Japan da masu bin tafarkin murdiya na kasar Jamus, na hadin gwiwa a kokarin mamaye duniya daga dukkan bangarorin gabas da yamma.
Yakin da Sinawa suka yi cikin adalci ya sa su samun karramawa, da goyon baya daga gamayyar kasa da kasa. Kana yadda al’ummun kasashe daban daban a wancan lokaci suka hada kai da juna a karkashin tutar yaki da tafarkin murdiya, ko da yake akwai bambanci a tsakaninsu ta fuskokin kasa, da kabila, da kuma akida, ya kai ga cimma nasara a yakin kin tafarkin murdiya, da tabbatar da sabon tsarin kasa da kasa bayan yakin a karshe.
Tarihin yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya ya nuna mana wasu tunani masu zurfi, wadanda jama’ar kasar Sin suka san su sosai:
Da farko dai, komai wahalhalun da aka sha, adalci zai yi galaba a kan muguntawa, haske kuma zai kori duhu. Wannan tamkar doka ce ta tarihi.
Na biyu, ‘yan Adam na da makomar bai daya. Ya kamata a samu daidaituwa, da jituwa, da cude-ni-in-cude-ka, tsakanin kasashe da kabilu daban daban, ta yadda za a samu damar tabbatar da tsaron bai daya, da kawar da yaki daga karshensa.
A zamanin da muke ciki, ana ta samun abkuwar rikice-rikice a duniya, inda dan Adam suka sake fuskantar bukatar yin zabi tsakanin cudanya da juna ko yin gaba da juna, zaman lafiya ko yaki. Sai dai kasar Sin ta riga ta samu babban ci gaba: Yanzu kasar na bikin tunawa da nasarar da ta samu ta gagarumin faretin soji. Kana a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, jama’ar kasar na ta kokarin zamanantar da kasarsu bisa hadin kansu.
Jawabin shugaba Xi Jinping ya bayyanawa duniya cewa: Kasar Sin mai karfi za ta ci gaba da samar da gudummawa ga ci gaban al’ummar dan Adam da na tattalin arzikin duniya cikin lumana.
Bari mu yi kokarin neman samun ci gaba tare, bisa wani tafarki na gaskiya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp