Kasar Sin da kungiyar tarayyar Afirka AU, sun yi alkawarin kara zurfafa hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare karkashin taron dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka FOCAC.
An yi alkawarin ne jiya Laraba a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, yayin wani taron karawa juna sani, inda jami’an kasar Sin da na kungiyar AU da kwararru suka tattauna gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani tare.
- Xi Ya Taya Trump Murnar Lashe Zaben Shugaban Amurka
- Mene Ne CIIE Ke Kawowa Kamfanonin Kasashen Waje?
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar AU Hu Changchun, ya ce, akwai bukatar Sin da Afirka su kara karfafa hadin gwiwarsu, da nufin kyautata jin dadin jama’ar Sin da Afirka, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
A nasa bangare kuwa, Khalid Boudali, shugaban majalisar tattalin arziki, zamantakewa da al’adu na kungiyar AU, cewa ya yi, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na ba da damar daukar matakan gudanar da harkokin mulki da ke karfafa jama’a da cibiyoyi na Afirka. (Yahaya)