Yayin da kasar Sin ke kara cika alkawuranta na fadada kawance da sauran sassan duniya, da burin kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, yanzu haka Sin din na kara dukufa wajen yaukaka kawance, musamman ma da abokan tafiyarta, wato kasashe masu tasowa. Tuni kasar Sin ta sha alwashin ci gaba da goyon baya, da amincewar juna tsakaninta da kasashen nahiyar Afirka, wadanda suka jima da zama abokan cimma moriya tare.
Yanzu haka dai sassan biyu na aiki tukuru, wajen karfafa hadin gwiwa a fannonin kirkire-kirkire, da wanzar da zaman lafiya da daidaito, da ingiza musayar al’adu, da sauransu.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-17 Dauke Da ’Yan Sama Jannati
- Jakadan Sin Mai Kula Da Shirin Kwance Damarar Makamai Ya Yi Kira Da A Tabbatar Da Ikon Kasashe Masu Tasowa Na Yin Amfani Da Kimiyya Da Fasaha Cikin Lumana
Karkashin hakan ne ma a baya bayan nan, kasar Sin ke kara azamar gudanar da ayyukan da suka kamata, na share fagen gudanar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, wanda zai gudana cikin shekarar 2024 dake tafe.
Tuni dai jagarorin kasashen Afirka suka yi na’am da wannan dandali, wanda karkashinsa sassan biyu ke aiki tukuru, wajen cimma burikansu na bunkasuwa bisa halin da suke ciki. Har ma a baya bayan nan aka jiyo mashawarcin shugaban kasar Senegal kan harkokin diflomasiyya mista Oumar Demba Ba, na jinjinawa kasar Sin bisa himmar ta wajen kafa wannan dandali na FOCAC, wanda ya ba da babbar gudummawar ingiza kawancen Afirka da Sin bisa mutunta juna, da kyautata abota, da amincewar juna da cimma moriya tare.
Ko shakka babu dandalin FOCAC ya dunkule sassan biyu, ya kuma samar da managarcin tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.
A gabar da ake dakon zagayowar lokacin gudanar da wannan muhimmin dandali, masharhanta na kara jinjinawa mashirya FOCAC bisa zurfin tunaninsu, wanda ya haifar da kafuwar sahihiyar dama ta tsara shirye-shirye, da manufofi na ingiza alakar diflomasiyya, da cinikayya, da tsaro, da hada hadar zuba jari, da kiwon lafiya, da yada ilimi da bincike, da musayar kwarewa da sanin makamar aiki, da sauran muhimman fannoni na ci gaban rayuwar bil Adama.
Fatan da duk mai burin ci gaban kasashe masu tasowa ke yi a wannan gaba, shi ne ganin bunkasar wannan dandalin na FOCAC, ta yadda zai ci gaba da dorewa bisa manufofinsa na alheri, masu yaukaka zumunta da haifar da gajiya ga kowa. (Saminu Alhassan)