• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Da Kasashen Nahiyar Afirka Na Kara Amincewa Da Juna

by Sulaiman
2 years ago
Sin

A baya bayan nan masharhanta na ci gaba da fashin baki kan yadda alakar kasar Sin da sauran kawayenta na Afirka ke kara yaukaka ta fannoni daban daban.

Ana kuma iya ganin shaidar hakan, idan aka dubi yadda manyan jami’an sassan biyu ke ta ziyartar juna, da tattaunawa, da kara jaddada burin kasashensu na karfafa cudanya da yin tafiya tare.

  • Sin Ta Samar Da Tallafin Jin Kai Na Gaggawa Sama Da 800 Ga Kasashen Waje Cikin Shekaru 5

Ko da a cikin makon nan ma yayin da shugaban zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji ke ziyarar aiki a kasar Senegal, ya jaddada manufar kasar Sin ta ci gaba da goyon bayan kasashen nahiyar Afirka, a fannin wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba.

Ko shakka babu, kasar Sin na nacewa matakan bunkasa alakarta da sauran kasashe masu tasowa, kamar yadda hakan ke gudana a zahiri, inda hadin gwiwar sassan a dukkanin matakai ke kara bunkasa yadda ya kamata.

A nasu bangare kuwa, kasashen Afirka na ta kara rungumar manufofin cimma moriyar juna tare da kasar Sin, karkashin shawarwari da manufofin da suka amincewa tare da kasar ta Sin. Karkashin hakan, kasashen Afirka da dama sun ci gajiya daga shawarar “ziri daya da hanya daya”, da manufofin samar da ci gaba da ake gudanarwa karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC da dai sauran su.

LABARAI MASU NASABA

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Don haka ne ma masu fashin baki ke ganin shaidun gani da ido sun riga sun tabbatar da aniyar Sin, na ci gaba da fadada hadin gwiwa da kasashen Afirka, da zurfafa musaya a fannonin raya al’adu, da ilimi, da kiwon lafiya.

Yayin da su kuma a nasu bangare, kasashen nahiyar ta Afirka ke fatan dorewar wannan kyakkyawar dangantaka, wadda ke haifar da tarin moriya ga al’ummun su. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
Daga Birnin Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Next Post
Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Modibbo Adama Ya Rasu

Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami'ar Modibbo Adama Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.