Kasar Sin da wasu kasashen tsakiyar Asiya biyar, sun lashi takobin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, a gabar da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na uku da ake kira (C+C5) a Kazakhstan.
Da yake jawabi a yayin taron manema labarai tare da mataimakin firaministan kasar Kazakhstan kana ministan harkokin wajen kasar Mukhtar Tleuberdi, Wang Yi ya bayyana sakamako da kuma matsayar da aka cimma a yayin taron.
A cewar Wang Yi, kasar Sin da wasu kasashen tsakiyar Asiya guda biyar, sun amince da kafa tsarin gudanar da taro a kai a kai tsakanin shugabannin kasashen Sin da kasashen yankin Asiya 5.
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasashen shida sun amince da kiyaye ka’idojin mutunta juna, da makwabtakar abokantaka mai kyau, da hadin kai a lokacin da aka shiga mawuyacin hali, da samun moriyar juna, don ciyar da yankin tsakiyar Asiya mai ‘yanci, da zaman lafiya, da wadata da hadin gwiwa gaba.